Gwamna Ya Gabatar da N40,000 a Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi? TUC Ta Yi Bayani
- Ana raɗe-raɗin Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya gabatar da N40,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata
- Kungiyar kwadago TUC reshen jihar Benuwai ta musanta raɗe-raɗin, ta ce har yanzu suna kan tattaunawa da wakilan gwamnati
- Shugaban TUC, Gideon Akaa ya ce har yanzu ba su cimma matsaya ba amma akwai N75,000 da N70,000 kan teburin tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Yayin da ake yaɗa jita-jitar cewa gwamnatin jihar Benuwai ta shirya biyan N40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, ƴan kwadago sun ce ba haka ba ne.
Shugaban kungiyar kwadago TUC reshen jihar Benuwai, Gideon Akaa, ya ce a yanzu haka suna kan tattaunawa da gwamnati kan sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Alia ya gabatar da N40,000?
Ya yi watsi da rahoton da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa gwamnatin jihar Benue ta gabatar da N40,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira ta wayar tarho ranar Juma'a, shugaban TUC ya ce har yanzu ba su cimma matsaya kan adadin sabon albashi mafi kankata ba.
Kwamared Akaa ya ce ƴan kwadago sun gabatar da N75,000 da N77,000 ga gwamnati a matsayin sabon albashin amma har yanzu ba a karkare tattaunawa ba.
Yan kwadago na tattaunawa da gwamnati
"Bani da masaniya game da jita-jitar N40,000, mun yi taro da gwamnati kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa. Babu wanda ya ambaci N40,000 a iya sanina.
"Daga ina wannan jita-jitar take fitowa dai ban sani ba, har yanzu gwamnati ba ta yanke adadin da za ta biya ba, idan mun gama tattaunawa kowa zai sani.
"Yayin da tattaunawar ke ci gaba da gudana, muna da alkaluma a ƙasa amma har yanzu ba mu amince da wani abu ba. Muna da N75,000, N77,000 a kan teburin tattaunawa.”
- Gideon Akaa.
Gwamna Uba zai biya N72,000 a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnatin jihar.
Uba ya amince da N72,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata wanda za a fara aiwatarwa daga watan Nuwamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng