'Yana Kwana babu Barci,' An Bayyana Ƙoƙarin da Tinubu Yake Yi Wajen Gyara Najeriya
- Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sunday Dare ya yi bayani kan abubuwa da suka shafi harkokin gudanar da gwamnati
- Dare ya bayyana yadda shugaban kasar ya ke matuƙar kokari wajen ganin Najeriya ta fita daga matsalar tattalin arziki
- Haka zalika ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri da cigaba da goyon bayan shugaba Tinubu har a cimma nasara a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yan Najeriya bayani a kan yadda shugaban kasa ke kokari.
Sunday Dare ya ce wahalhalun da ake ciki za su wuce domin Mai girma Bola Tinubu na matuƙar ƙoƙarin kawo ƙarshensu.
Legit ta tatttaro bayanan da Sunday Dare ya yi ne a cikin wani bidiyo da Channels Television ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Bola Tinubu ke aiki cikin dare
Sunday Dare ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana matuƙar ƙoƙari wajen kawo karshen matsalolin Najeriya.
"Mutum ne wanda yake aiki har cikin dare a lokacin da sauran mutane marasa hazaƙa ke barci.
"Na yi aiki da shi (Bola Tinubu) na tsawon shekaru bakwai, ba mu barci har sai karfe 4, 5 ko 6 na safe."
- Sunday Dare, Hadimin shugaban kasa
Maganar cire tallafin man fetur
Sunday Dare ya bayyana cewa Bola Tinubu ya yi kokari wajen cire tallafin man fetur kasancewar shugabanni da dama sun gaza hakan.
Dare ya kara da cewa duk da ana shan wahala a gaba kadan za a samu riba idan abubuwa suka daidaita.
Tinubu: Dare ya ba yan Najeriya hakuri
Sunday Dare ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri kan halin kunci da suke ciki saboda wasu tsare tsaren gwamnati.
Ya kara da cewa yanzu haka ba a cika shekaru biyu ba kuma nan gaba kadan tsare tsaren gwamnati za su fara amfanan yan kasa.
Tinubu ya yi martani ga gwamnonin Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani ga gwamnonin Arewa kan adawa da sabuwar dokar haraji.
Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya sun yi taro ranar Litinin inda suka yi fatali da dokar haraji da Bola Tinubu ke shirin kawowa Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng