Kwana Ya Kare: Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Rasu a Hatsari

Kwana Ya Kare: Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Rasu a Hatsari

  • Allah ya yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Christopher Ayeni rasuwa ranar Alhamis
  • Tsohon ɗan majalisar ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin motar da ya rutsa da shi a kan titin Ilorin zuwa Ajase a jihar Kwara
  • Hukumar kiyaye haɗurra FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ɗan siyasar ya cika ne bayan an isa asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara - Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Christopher Ayeni ya rasu ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, 2024.

Honorabul Ayeni ya mutu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a titin Ilorin zuwa Ajase da ke ƙaramar hukumar Irepodun a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

An ƙara babban rashi a Najeriya, tsohon ɗan Majalisa ya riga mu gidan gaskiya

Hon. Christopher Ayeni.
Tsohon kakakin majalisar dokokin Kwara, Christoher Ayeni ya rasu a hadarin mota Hoto: Solomon Ademola Owosho
Asali: Facebook

Tsohon ɗan majalisa ya rasu a hatsari

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da wata motar haya mai lamba T-17488LA da motar Toyota Hilux mai lamba ARP545KY.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin wanda ya zama ajalin tsohon ɗan majalisar ya auku ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Alhamis.

FRSC ta faɗi abin da ya faru a hatsarin

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kwara ta tabbatar da afkuwar hatsarin a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Basambo Olayinka.

Sanarwar ta ce mutane biyar ne suka jikkata a hadarin, sai dai daga baya Hon. Christopher Ayeni ya rasu a asibiti.

Gwamnan Kwara ya miƙa sakon ta'aziyya

Tuni dai gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya jajantawa 'yan uwa, abokan arziki da makusanta bisa rasuwar Ayeni, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin lantarki: Yan Arewa sun tafka asara, an rasa sama da Naira tiriliyan 1

Gwamnan, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya bayyana lamarin a matsayin mai muni.

AbdulRazaq ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga al’ummar garin Isapa da ke karamar hukumar Ekiti kan wannan babban rashi na ɗansu da suka yi.

Gwamnan ya roki Allah Madaukakin Sarki ya ji kan tsohon dan majalisar ya kuma bai wa iyali, ƴan uwa da masoya karfin ikon jure wannan babban rashi.

Tsohon ɗan majalisa ya rasu a Ibadan

A wani rabarin, kun ji cewa shugaban hukumar kula da walwalar al'umma ta jihar Oyo, OYCSDA, Hamid Babatunde Eesuola ya rasu a asibitin UCH da ke Ibadan.

Rahotanni sun nuna cewa Hamid Babatunde, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Oyo ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262