An Yi Barnar Asarar Rayuka bayan 'Yan Banga Sun Fafata da 'Yan Bindiga

An Yi Barnar Asarar Rayuka bayan 'Yan Banga Sun Fafata da 'Yan Bindiga

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Dogon Ruwa na ƙaramar hukumar Wase ta jihar Plateau
  • Ƴan bindigan da suka je da niyyar yin garkuwa da mutane sun fuskanci turjiya daga wajen jami'an tsaro na ƴan banga
  • A yayin artabun da suka yi, an rasa rayukan mutum huɗu da suka haɗa da ƴan bindiga uku da ɗan banga guda ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan banga sun yi musayar wuta da ƴan bindiga a jihar Plateau.

Aƙalla mutane huɗu ne suka rasu a arangamar da aka yi tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a ƙauyen Dogon Ruwa da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

'Yan bindiga sun fafata da 'yan banga a Plateau
'Yan banga sun yi artabu da 'yan bindiga a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani shugaban matasa kuma ɗan banga a garin, Abdullahi Shu'aibu ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙauyukan Wase dai sun sha fuskantar hare-haren ƴan bindiga a cikin shekar biyu da suka gabata, wanda hakan ya yi sanadiyyar hallaka mutane da sace wasu.

Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga

Abdullahi Shu'aibu ya bayyana cewa ƴan bindigan sun je garin ne da niyyar yin garkuwa da mutane, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da hakan.

"Ƴan bindigan sun iso ƙauyen ne da nufin yin garkuwa da mutanen. Sun ajiye baburansu a kusa da ƙauyen amma mun samu labarin shirinsu."
"Ƴan bindigan sun shiga gidaje, inda suke zaɓar wadanda za su yi garkuwa da su, ba tare da sanin cewa ‘yan banga na can sun yi lamɓo a kusa da baburansu ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace manoma suna tsaka da girbi a gonakinsu

"A yayin da suke yunƙurin tafiya da mutanen da suka sace, ƴan banga sun farmake su inda suka kashe ƴan bindiga uku. Abin takaici, an kuma kashe ɗan banga guda ɗaya.”

-.Abdullahi Shu'aibu

Ƴan bindiga sun kai hari a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga suka kai a garin Anyiin da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.

Ƴan bindigan sun mamaye garin ne a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024 da misalin ƙarfe 6:32 na yamma, inda suka kashe mutane da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng