Gwamnatin Tinubu Ta kawo Hanyar da Arewa Za Ta Rage Samun Rashin Wuta

Gwamnatin Tinubu Ta kawo Hanyar da Arewa Za Ta Rage Samun Rashin Wuta

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana kan lalacewar wutar lantarki a Arewacin Najeriya da hanyar da za a samu mafita
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi bayanai da ya kawo wata ziyara jihar Kano bayan wuta ta dawo a Arewa
  • Adebayo Adelabu ya gana da kamfanin rarraba wuta na KEDCO kuma ya yi masa kira na musamman kan raba lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ministan makamashin Najeriya, Adebayo Adelabu ya kai wata ziyarar aiki Kano a yau Alhamis, 31 ga Oktoba.

Cif Adebayo Adelabu ya yi kira ga gwamnonin Arewa kan samar da tashoshin wutar lantarki a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Sai bayan mako 2: An ƙara shiga ruɗani kan wutar Arewa

Ministan wuta
Ministan makamashi ya ziyarci Kano. Hoto: @Bayoadelabu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ministan ya gana da kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO yayin ziyarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyar rage shiga rashin wuta a Arewa

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Arewacin Najeriya ya dogara ne sosai da layukan wuta da ke Shiroro da Jos.

Adelabu ya ce hakan na nufin yankin Arewa zai iya fuskantar barazanar lantarki idan layukan wutar suka samu matsala amma akwai mafita.

"Mafita ita ce gwamnonin jihohin Arewa su samar da wuta ta kansu saboda kaucewa bacin rana.
Hakan zai zamo hanya da yankin Arewa zai kaucewa shiga duhu idan aka samu lalacewar manyan layukan wutar."

-Adebayo Adelabu

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin ɗaukar matakai domin kaucewa daukewar wuta gaba daya idan tushen lantarki na kasa ya samu matsala.

The Guardian ta ce Adelabu ya kuma yi kira ga kamfanin rarraba wuta na KEDCO kan ya rika kokarin tabbatar da cewa yankuna sun samu lantarki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Gwamnatin Tinubu ta fadi lokacin gyara lantarkin Arewa

Minista ya yi magana kan wutar Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kara bayani kan lokacin da wutar lantarki za ta kammala dawowa a jihohin Arewacin Najeriya.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa sai ranar 12 ga watan Nuwamba za a kammala gyaran wutar Arewa.

Ana sa ran cewa da zarar kamfanin TCN ta kammala gyaran za a samu cikakkiyar wuta a dukkan jihohin Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng