'Ku Taimake Mu': Gwamna Ya Nemi Alfarmar Malaman Addini, Ya Fadi Tasirinsu

'Ku Taimake Mu': Gwamna Ya Nemi Alfarmar Malaman Addini, Ya Fadi Tasirinsu

  • Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya nemi alfarmar malaman addini wurin taya shi da addu'o'i a gwamnatinsa
  • Gwamna Oborevwori ya bayyana haka ne a gidan gwamnati inda ya ce ba zai lamunci ayyuka marasa inganci ba
  • Gwamnan ya bayyana irin gudunmawa da malaman addini suke ba shi wurin inganta rayuwar al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya bayyana himmatuwar gwamnatinsa wurin inganta rayuwar al'umma.

Gwamna Oborevwori ya ce yana iya bakin kokarinsa wurin tabbatar da cika alkawuran da ya dauka.

Gwamna ya bukaci alfarmar malaman addini a gwamnatinsa
Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana tasirin malamai a gwamnatinsa. Hoto: Sheriff Oborevwori.
Asali: Twitter

Gwamna ya tuno muhimmancin malaman addini

Oborevwori ya fadi haka ne yayin karbar bakoncin malaman addinin Kirista a gidan gwamnatin jihar, cewar AIT News.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana muhimmancin malaman addinin wurin cigaban da gwamnatinsa ta samar a jihar Delta.

Ya ce ba zai lamunci yin ayyuka marasa inganci ba daga yan kwangila yayin gudanar da ayyukansu.

Har ila yau, Gwamna Oborevwori ya bukaci addu'o'i daga Fastocin domin samun cigaba a gwamnatinsa.

Fasto ya yabawa Gwamna kan ba su mukamai

Shugaban cocin Isoko, Bishop Aruakpor ya yabawa Gwamna Oborevwori kan irin ayyukan cigaba da yake yi a jihar.

Aruakpor ya ce ba za su manta da nadin mukamai da ya ba yan yankin Isoko a kokarin kawo daidaito a jihar.

Daga bisani ya Faston ya ba gwamnan tabbacin ba shi goyon baya dari bisa dari kan ayyukan alheri da ya ke yi inda ya ce yana kan hanya madaidaiciya.

Gwamna ya umarci biyan mafi ƙarancin albashi

Kun ji cewa Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ya umarci fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 ga mafi ƙanƙantan ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

'Muna tausaya muku': Gwamnonin APC sun magantu kan halin kunci, sun ba da tabbaci

Gwamna Sheriff ya ba da umarnin biyan ne nan take wanda za a fara ba ma'aikata a karshen watan Oktoban 2024 da muke ciki.

Sakataren gwamnatin jihar ya tabbatar da haka, ya ce gwamnan ya duba halin da al'umma ke ciki ne na tsadar rayuwa a yau bayan cire tallafin man fetur a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.