Gwamnatin Tinubu Ta Jiƙa Ƴan Najeriya da Kudi, Mutum Miliyan 25 Sun Samu N25,000
- Gwamnatin tarayya ta ce zuwa yanzu ta turawa ƴan Najeriya miliyan 25 har N25,000 domin rage raɗaɗin halin da ake ciki
- Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan taron majalisar tattalin arziƙi NEC
- Edun ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakai daban-daban donn ragewa jama'a raɗaɗin cire tallafin mai da aka yi a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa akalla ƴan Najeriya miliyan 25 sun samu tallafin rage raɗaɗi (CCT) na N25,000.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis bayan taron NEC.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki watau NEC a Aso Villa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin jihohi 36, ministoci da manyan jami'an gwamnatin tarayya na cikin ƴan majalisar NEC ta ƙasa.
Gwamnatin Tinubu ta tallafawa ƴan Najeriya
Da yake jawabi bayan taron, Edun ya lissafo matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka domin ragewa ‘yan Najeriya raɗadin wahalhalun da aka shiga sakamakon cire tallafin mai.
Ministan ya ƙara da cewa magidanta akalla miliyan biyar ne suka amfana da wannan tallafin kudi na N25,000 kai tsaye ba tare da shamaki ba.
Ya kuma bayyana cewa a cikin kwanaki biyar da suka gabata, an rabawa mutane 11,000 kudi Naira biliyan 3.5 a tsarin bashi na mabukata.
Yadda dalibai suka samu rancen kuɗi
Wale Edun ya kuma ce kawo yanzu an tura kuɗi sama da biliyan 90 ga daliban Najeriya 500,000 a karkashin shirin rancen dalibai, rahoton Punch.
Ya ce wannan na daga cikin irin matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka da nufin sauƙaƙawa ƴan Najeriya duba da tsadar rayuwar da ake ciki.
Wata mata, Asiya Ahmad ta tabbatarwa wakilin Legit Hausa cewa an tura mata N25,000 daga gwamnatin tarayya.
"Eh ni ma an bani, kuɗin sun mani amfani gaskiya kuma na ji ance sau uku a za bayar amma ha yanzu shiru. kudin suna rage mana wani abun."
"Ina kira ga gwamnati ta ƙara zage dantse, ta ɓullo da matakan yayewa ƴan Najeriya wahalar da ake ciki.
Tinubu ya maida martani kan tsarin VAT
A wani rahoton, an ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani kan kokarin gwamnonin Arewa na kawo cikas ga sabuwar dokar haraji da Bola Tinubu ke son kawowa.
Gwamnatin tarayya ta ce Bola Tinubu ba shi da niyyar cutar wani yanki na Najeriya a cikin sabon tsarin haraji da ya yi niyyar kawowa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng