Tinubu Ya yi Martani bayan Gwamnonin Arewa Sun Fara Yaƙar Tsarin Harajinsa
- Fadar shugaban kasa ta yi martani kan kokarin gwamnonin Arewa na kawo cikas ga sabuwar dokar haraji da Bola Tinubu ke son kawowa
- Gwamnatin tarayya ta ce Mai girma Tinubu ba shi da niyyar cutar wani yanki na Najeriya a tsarin haraji da ya yi niyyar samarwa
- A ranar Litinin, 28 ga Oktoba gwamnoni da sarakunan Arewa suka yi taro kuma suka sanar da kin amincewa da sabon tsarin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan sukan da gwamnonin Arewa suka yi wa dokar da Bola Tinubu ke shirin kawowa.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tura bukatar sauya fasalin haraji ne ga majalisa amma gwamnonin Arewa suka nuna adawa da ita.
Legit ta tatttaro martanin da fadar shugaban kasa ta yi ne a cikin wani sako da hadimin Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maratanin Bola Tinubu ga gwamnonin Arewa
Fadar shugaban kasa ta mika godiya ga gwamnoni da sarakunan Arewa kan yadda suke ba da hadin kai wajen yaki da yan ta'adda.
Bayan haka, fadar shugaban kasa ta bukaci gwamnonin Arewa da su fahimci cewa dokar da Tinubu ke son kawowa ba za ta cutar da yankinsu ba.
Bola Tinubu ya ce a halin yanzu dole ne a yi gyara a kan yadda ake tattara haraji a kasa kuma ka da wani yanki yaji kamar ana faɗa da shi ne.
Dokokin haraji da Tinubu ya kai majalisa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika kudurin haraji hudu ne a gaban majalisa da niyyar sauya fasalin tattara haraji a fadin Najeriya.
Bola Tinubu ya ce dokokin za su kawo gyare gyare a kan yadda ake tattara haraji a Najeriya wanda idan ba a yi haka ba za a cigaba da yin kuskure.
Duk da sukar da gwamnonin suka yi, Bola Tinubu ya ce babu wani lokaci da ya kamata majalisa ta amince da kudirorin harajin kamar yanzu.
NLC ta yi martani bayan karin kudin mai
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta dura kan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan karin kudin man fetur a ranar Talata.
Kungiyar kwadago ta ce karin kudin man fetur a lokacin da talaka ke fama da matsalar tattalin arziki zai iya haifar da rikici a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng