An Kama Ɗan Bindigar da Ya Kashe Basarake bayan Karɓar Miliyoyi

An Kama Ɗan Bindigar da Ya Kashe Basarake bayan Karɓar Miliyoyi

  • Rahotanni na nuni da cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wani dan bindiga da ake zargi da garkuwa da mutane
  • Matashin mai suna Nasiru Sanusi ya yi yawo a jihohi da dama yana ta'addanci kafin yan sanda su yi haɗaka wajen cafke shi a Gombe
  • Jami'an yan sandan reshen jihar Katsina sun bayyana yadda dan bindigar ya kashe wani basarake bayan ya karbi kudin fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da garkuwa da mutane.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan sanda sun kama matashin da ake zargin ne a ranar 23 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Kaico: Wani matashin yaro ɗan shekara 16 ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa

Katsina
An kama dan bindiga da ya kashe sarki. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Channels Television ya nuna cewa matashin ya yi garkuwa da wani basarake kuma ya kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan bindiga ya yi garkuwa da basarake

Daily Post ta wallafa cewa an kama wani matashi mai suna Nasiru Sanusi da ake zargi da jagorantar garkuwa da wani basarake.

Ana zargin cewa Nasiru Sanusi ya haɗa kai da wasu mutane uku suka yi garkuwa da baffansa wanda shi ne sarkin kauyensu.

Biyo bayan haka, sai suka bukaci kudin fansa N8m da buhunan taki shida wanda bayan an ba su kudin suka kashe basaraken.

Yadda aka kama dan bindiga a Gombe

Rahotanni na nuni da cewa matashin dan asalin kauyen Gidan Daudu ne a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Bayan kashe basaraken ne Nasiru ya gudu, daga nan yan sanda a Katsina suka hada kai da jami'an Gombe aka kama shi.

Kara karanta wannan

'A bar mutane su mallaki bindiga domin maganin yan ta'adda,' Sanata

Jihohin da Nasiru ya yi ta'addanci

Yayin da ake bincikensa, Nasiru Sanusi ya bayyana cewa ya yi yawon ta'addanci a jihohin Gombe, Taraba da Legas.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa za ta cigaba da bincike domin gano sauran miyagun da Nasiru ya hada baki da su wajen kashe basaraken.

Yan bindiga sun kashe dan kasuwa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta tabbatar da kisan gilla da aka yi wa wani dan kasuwa mai shekaru 48, Micheal Nnaji.

Lamarin ya faru ne a wani yanki na ƙaramar hukumar Ohauku yayin da wasu yan bindiga suka kai masa hari da misalin karfe 9:45 na dare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng