An Ƙara Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Ɗan Majalisa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Shugaban hukumar kula ada walwalar al'umma ta jihar Oyo, OYCSDA, Hamid Babatunde Eesuola ya rasu a asibitin UCH da ke Ibadan
- Rahotanni sun nuna cewa Hamid Babatunde, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Oyo ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Makusantan marigayin sun ce a halin yanzu an fara shirye-shiryen dawo da gawarsa gida domin yi masa jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Atiba a majalisar dokokin jihar Oyo, Hon. Hamid Babatunde Eesuola ya riga mu gidan gaskiya.
Eesuola wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da walwala da jin daɗin al’umma ta jihar (OYCSDA) ya rasu ne a Ibadan, babban birnin Oyo.
Yaushe tsohon ɗan majalisar ya rasu?
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa tsohon ɗan majalisar ya rasu ne yau Alhamis, 31 ga watan Oktoba, 2024 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban kungiyar tsofaffin daliban makarantar Alaafin na kasa, Engr. Seun Adesiji shi ne ya tabbatar da rasuwar Hamid Eesuola.
“Eh, zan iya tabbatar da cewa Hon. Hamid Babatunde Eesuola ya rasu a safiyar yau Alhamis a Ibadan.
"Makusantansa sun tabbatar mani da cewa an ɗauko gawarsa zuwa gida domin yi masa jana’iza, ina jiran su ƙariso nan ba da jimawa ba domin na bi su,” in ji Adesiji.
Adesiji ya ce marigayin wanda jigo ne a PDP ya faɗawa abokansa cewa maƙogwaronsa na masa ciwo a makon da ya gabata.
An fara shirin yi masa jana'iza ta Musulunci
Daya daga cikin abokan siyasarsa, Kayode Oladoku ya tabbatar da rasuwar Eesuola a asibitin Jami’a (UCH) da ke Ibadan.
Oladokun ya kara da cewa yanzu ya bar gidan marigayin inda ake shirye-shiryen yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Bsyanai sun nuna cewa na shirya tsohon ɗan majalisar zai kare kare kundin karatunsa a jami'ar Ibadan, inda ya kammala karatun digiri na uku watau Ph. D.
Mahaifiyar sarki ta rasu a Ogun
A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yiwa mahaifiyar sarkin masarautar Owu da ke Abeokuta, jihar Ogun, Oba (Farfesa) Saka Adelola Matemilola rasuwa.
An rahoto cewa Alhaja Alirat Ayinke Matemilola, mahaifiyar sarkin ta rasu tana da shekaru 81 a ranar Lahadi, 27 ga Oktoba.
Asali: Legit.ng