"Kar Ku Ji Komai:" Yan Kasuwa Sun Yi Martani bisa Fargabar Karancin Fetur

"Kar Ku Ji Komai:" Yan Kasuwa Sun Yi Martani bisa Fargabar Karancin Fetur

  • Kungiyar Energies Marketers Association of Nigeria da ke kasuwancin fetur ta ce babu kamshin gaskiya a cewa za a yi karancin mai
  • Shugaban kungiyar na kasa, Mista Clement Isong ya shawarci jama'a da su yi watsi da labarin kuma su daina sayen fetur don boyewa
  • Da ya ke ba da tabbacin, Isong ya ce yanzu 'yan kasuwa na da dabarar wadata abokan huldarsu tun bayan yi wa sashen garanbawul

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siya

Jihar Lagos - Kungiyar yan kasuwa ta Energies Marketers Association of Nigeria (MEMAN) ta yi martani a kan fargabar za a samu karancin fetur.

Kara karanta wannan

Fetur: 'Yan kasuwa sun maidawa Dangote amsa, sun fadi halin da kasuwa ke ciki

Shugaban MEMAN na kasa, Clement Isong ne ya bayyana haka a jihar Legas a ranar Alhamis, inda ya kwantarwa da jama'a hankali.

Fetur
MEMAN ta ce ba za a yi karancin fetur ba Hoto: Kypros/Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ba za a samu karancin man fetur kamar yadda wasu ke fargabar zai afku ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MEMAN ta ce akwai fetur a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan kasuwa sun musanta labarin cewa za a fuskanci karancin man fetur a fadin kasar nan.

Shugaban MEMAN, Mista Clement Isong ya shawarci mazauna Najeriya da ka da su rika sayen fetur su na boyewa saboda fargabar.

"Ba za a samu karancin fetur ba:" MEMAN

Kungiyar yan kasuwar man fetur na kasar nan (MEMAN), ta ce zai yi wahala a samu karancin man fetur a fadin Najeriya.

Shugaban MEMAN, Clement Isong ya ce tun bayan da gwamnati ta tsame kanta daga harkar fetur yan kasuwa su ka rika sayo fetur domin ajiya.

Kara karanta wannan

'APC ta shiga uku': An ci gyaran Tinubu kan korar Minista, an fada masa illar hakan

Ghana na son fetur daga Najeriya

A wani labarin kun ji cewa mahukunta a kasar Ghana sun bayyana sha'awar dakon fetur daga matatar Dangote bayan shugaban kamfanin, Aliko Dangote ya ce ana fitar da ganga 650,000 a kullum.

Shugaban hukumar kula da sha’anin man fetur na Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya ce kasarsa za ta gwammace ta rika sayo fetur daga matatar Dangote maimakon daukowa daga Turai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.