'Yan Kasuwa Sun Bi Sahun NNPCL, Sun Kara Farashin Man Fetur a Najeriya
- Ƴan kasuwa sun ƙara farashin man fetur kwanaki kaɗan bayan gidajen man NNPCL sun yi ƙari a Najeriya
- Farashin litar mai a gidajen man ƴan kasuwa masu zaman kansu ya tashi daga N1,060 zuwa tsakanin N1,100 da N1,200
- Legit Hausa ta zanta da wani ma'aikacin gidan mai a Kaduna, wanda ya tabbatar da wannan ƙari da aka samu a makon nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan tsadar rayuwa, ƴan kasuwar mai sun ƙara farshin litar man fetur a faɗin ƙasar nan.
Dillalan man sun kara farashin kayansu ne kwanaki ƙalilan bayan kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya ƙara tashin farashin litar mai a gidajen mansa.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa manyan ƴan kasuwa sun ƙara farashin litar fetur daga N1,010 zuwa N1,050 a Legas da yankunan da ke kewaye ta ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na nufin dai an samu karin kashi 4% a farashin da man, wanda ba zai yi wa mutane daɗi ba duba da halin kuncin da ake ciki.
Farashin fetur ya haura N1,100 a Najeriya
A ɗaya ɓangaren kuma ƴan kasuwa masu zaman kansu sun ƙara tsadar litar mai daga N1,060 zuwa tsakanin N1,100 da N1,200 ya danganta da yanki, Channels tv ta kawo.
An tattaro cewa sakamakon sakin ragamar kayyade farashi ga yanayin kasuwa, babu mai ƙayyade farashi guda ɗaya sai yadda kasuwa ta kama.
Wannan ya sa a yanzu ake samun banbancin farashi a tsakanin gidajen mai, wasu kuma farashinsu iri ɗaya.
"Fetur ya ƙara tsada a wannan makon"
Wakilin Legit Hausa ya ziyarci wani gidan mai a Marabar Ɗanja da ke yankin ƙaramar hukumar Kudan a jihar Kaduna, inda ya sayi fetur a farashin N1,200.
Ma'aikacin gidan man wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida mana cewa a makon nan farashin ya ƙaru daga N1,100 zuwa N1,200.
"Kwanan nan aka samu kari, ba zan ce maka ga dalili ba amma daga sama aka kira mu aka bamu umarnin ƙara farashin zuwa N1,200."
"Mutane sun fara gajiya, yanzu adadin litar man da muke sayarwa a kullum ya ragu, galibi yanzu an koma sai buƙata ta zama dole ake sayen mai. Muna fatan Allah ya kawo mana sauki," in ji shi.
IPMAN ta maida martani ga Ɗangote
A wani rahoton kun ji cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa, (IPMAN) ta bayyana mamakin yadda matatar Dangote ta ce an ki sayen fetur daga wurinta.
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce akwai litar fetur miliyan 500 a ajiye, matatarsa na fitar da lita 650,000 kullum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng