'Muna Tausaya Muku': Gwamnonin APC Sun Magantu kan Halin Kunci, Sun ba da Tabbaci

'Muna Tausaya Muku': Gwamnonin APC Sun Magantu kan Halin Kunci, Sun ba da Tabbaci

  • Gwamnonin Najeriya sun bayyana tasirin tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu yayin da ake cikin halin kunci a ƙasar
  • Shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce suna tausayawa yan Najeriya kan halin da ake ciki
  • Hakan ya biyo bayan taro na musamman da gwamnonin suka yi a Abuja a jiya Laraba 30 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar gwamnonin Najeriya ta nuna damuwa kan halin da yan kasar ke ciki na matsin rayuwa.

Ƙungiyar ta tabbatar da cewa ana cikin wani hali inda ta ba da tabbacin cewa Bola Tinubu yana iya bakin kokarinsa.

Gwamnonin APC sun ba da tabbacin samun sauki kan tsare-tsaren Tinubu
Gwamnonin APC sun yabawa tsare-tsaren Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Halin kunci: Gwamnonin APC sun ba da tabbaci

Kara karanta wannan

Kuncin rayuwa: Gwamnoni, sarakuna sun shiga ganawa da Tinubu

Shugaban gwamnonin APC, Gwamna Hope Uzodinma shi ya bayyana haka a yau Alhamis 31 ga watan Oktoban 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hope Uzodinma ya ce yana da tabbacin Bola Tinubu ya shirya kawo karshen halin da ake ciki a fadin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan halin kunci da aka jefa al'umma tun bayan cire tallafi man fetur a Najeriya.

Gwamna Uzodinma ya ce sun yi ganawa da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari kan cire tallafin mai gaba daya da kuma kalubalen da suke fuskanta.

Gwamnonin APC sun yabawa tsare-tsaren Bola Tinubu

"Sauki na nan tafe ba da jimawa ba, muna tausayawa talakawa kan halin da suke ciki."
"Muna godiya da irin matakan da Tinubu ke dauka domin kawo sauyi a Najeriya baki daya."
"Muna fatan sauki zai samu nan ba da jimawa ba domin girban tsare-tsaren da Tinubu ya ke aiwatarta a kasar."

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya dauki mataki da matashi ya yi zargin ya kware a neman mata

- Hope Uzodinma

Gwamnoni sun bukaci ba sarakunan gargajiya dama

Kun ji cewa an yi taro tsakanin gwamnonin jihohi da sarakunan gargajiya a birnin Abuja a jiya Laraba 30 ga watan Oktoban 2024.

Gwamnonin sun bukaci ba sarakunan dama a kundin tsarin mulki domin ba da gudunmawa a bangarori da dama da suka hada da zaman lafiya da tsaro.

A cewarsu, daukar matakin zai taimaka sosai wurin inganta shugabanci da samar da tsaro da kuma dakile sauran matsaloli.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.