'Gwamnati na Hura Wutar Rikici,' NLC Ta yi Gargadi kan Karin Kudin Fetur

'Gwamnati na Hura Wutar Rikici,' NLC Ta yi Gargadi kan Karin Kudin Fetur

  • Kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da karin kudin man fetur da aka samu a faɗin Najeriya a ranar Talata da ta gabata
  • Yan kwadago sun nuna takaici kan yadda ake cigaba da samun karin kudin man fetur duk da wahalar rayuwa da ake ciki a Najeriya
  • Legit ta tattauna da wani mai sana'ar acaba domin jin yadda suke fama da mutane bayan karin kudin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta fusata bayan an samu karin kudin man fetur a fadin Najeriya.

Yan kwadago sun ce bai kamata a samu karin kudin fetur ba lura da yadda ake fama da wahalar rayuwa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kwastam ta damke fetur na miliyoyin kudi ana shirin safararsa zuwa ketare

Yan kwadago
Yan kwadago sun yi Allah wadai da karin kudin fetur. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Wani jigo a kungiyar kwadago ne ya zanta da jaridar Vanguard bayan an samu karin kudin fetur a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar NLC ta soki karin kudin man fetur

Kungiyar kwadago ta bayyana cewa karin kudin fetur da aka yi a ranar Talata kokari ne na kure hakurin talakawan Najeriya.

Yan kwadago sun ce sam bai kamata mutane na fama da wahalar rayuwa ba sannan a rika kara jefa su cikin karin wahalhalu.

Fetur: Ana hura wutar rikici inji NLC

Bayan karin kudin mai, yan kwadago sun ce gwamnatin tarayya ta tara makamashin hura wutar rikici a Najeriya.

Economic Confidential ta wallafa cewa NLC ta ce ana jiran wanda zai ƙyasta wutar rikici ne kawai Najeriya ta birkice saboda wahalar rayuwa.

Kungiyar ta ce duk wanda aka kure dole zai yi kokarin ɗaukar wani mataki kuma abin da zai iya faruwa a Najeriya kenan.

Kara karanta wannan

"Kar ku ji komai:" Yan kasuwa sun yi martani bisa fargabar karancin fetur

"Muna ta tunanin cewa gwamnati za ta yi amfani da hankali ta tausayawa al'umma amma abu ya gagara.
Muna jin tsoron halin da za a shiga a Najeriya idan lamarin ya cigaba da tafiya a haka, domin ana son kure talakawa."

- Yan kwadago

Legit ta tattauna da dan acaba

Wani dan acaba mai suna Muhammad Ibrahim ya bayyanawa Legit cewa karin kudin man fetur yana kara jefa su a matsala.

Muhammad Ibrahim ya ce mutane suna yawan rokon a musu sauki alhali kudin mai ya karu kuma yawanci idan ba a dauke su ba yawo za a ta yi ba a samu wasu ba.

Oshiomhole ya bukaci karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa Adams Oshiomhole ya bukaci a yi karin albashi ga ma'aikatan Najeriya a kan N70,000.

Sanata Adams Oshiomhole ya ce yana da matuƙar kyau a yi karin albashi idan aka lura da yadda ake wahala a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng