'Yan Kasuwa Sun Fadi Dalilin Kasa Fara Jigilar Fetur daga Matatar Dangote
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta yi ƙarin haske kan dalilin kasa fara ɗauko fetur daga matatar Dangote da ke Legas
- IPMAN ta hannun kakakinta ta bayyana cewa har yanzu suna kan tattaunawa ne da matatar Dangote kan yadda tsarin zai kasance
- Ta bayyana cewa har yanzu ƴan kasuwa ba su fara samun fetur ba daga matatar Dangote amma an kusa kammala tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Ƙungiyar dillalan man fetur ta IPMAN, ta yi magana kan dalilin kasa fara jigilar fetur daga matatar Dangote.
Ƙungiyar IPMAN ta bayyana cewa har yanzu suna kan tattaunawa da matatar Dangote kan sharuɗan fara jigilar man.
Jami'in hulɗa da jama’a na ƙungiyar IPMAN, Cif Chinedu Ukadike, ya shaidawa jaridar Vanguard halin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin yake cewa har yanzu ƴan kasuwa ba su fara ɗauko fetur kai tsaye daga matatar Dangote ba.
Dalilin kasa jigilar fetur daga matatar Dangote
Ya ƙara da cewa a halin yanzu suna ci gaba da tatttaunawa da matatar kan yadda tsarin zai kasance.
"Har yanzu ba mu fara samun fetur daga matatar Dangote ba, amma ana kan hanyar yin hakan. Zan sanar da ku da zarar an kammala komai."
"Har yanzu ba a fara ba ƴan kasuwa fetur ba. Ina tunanin Dangote yana amfani da wani salon kasuwanci ne amma muna ci gaba da tattaunawa."
- Cif Chinedu Ukadike
Dangote ya yi kira ga NNPCL da ƴan kasuwa
Kalaman nasa na zuwa ne bayan Dangote ya yi kira ga kamfanin NNPCL ƴan kasuwa da su daina shigo da fetur daga ƙasashen waje.
Dangote ya bayyana cewa matatarsa tana da fetur da zai wadaci ƙasar nan ba sai an shigo da shi daga waje ba.
Dangote ya ba gwamnati shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote, ya ce akwai bukatar Najeriya ta daina jinginar da danyen mai domin tabbatar da samuwar man ga matatun cikin gida.
Dangote ya nuna takaici kan yadda Najeriya ke amfani da danyen man da ko hakoshi ba a yi ba wajen karba da biyan basussuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng