Haraji: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Martani ga Gwamnonin Arewa, Ta Fadi Tsare Tsarenta
- Yayin da gwamnoni ke korafi kan kudirin haraji a gaban Majalisar Tarayya, Gwamnatin Bola Tinubu ta yi martani
- Gwamnonin sun ki amincewa da kudirin rarraba harajin VAT da ke gaban Majalisar, suka ce akwai rashin adalci
- Sai dai shugaban kwamitin kudi da inganta haraji, Taiwo Oyedele ya ce babu rashin adalci a cikin tsarin dokar harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani ga gwamnonin Arewa kan maganar haraji.
Shugaban kwamitin Gwamnatin Tarayya na kudi da inganta haraji, Mr Taiwo Oyedele ya ce an yi adalci kan kudirin harajin.
Harajin Tinubu: Gwamnoni sun yi fatali da tsarin
Daily Trust ta ce Oyedele ya yi martani ne ga gwamnonin da suka ki amincewa da kudirin harajin da ke gaban Majalisar Tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan kin amincewa da gwamnonin jihohi 19 na Arewa suka yi kan tsarin rarraba harajin VAT a kasa.
Shugaban gwamnonin, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, ya ce sun ki amincewa ne saboda zai sake durkusar da al'umma.
Inuwa ya bukaci Majalisar Tarayya da kudirin ke gabanta ta yi farali da shi saboda halin da al'umma ke ciki, cewar Premium Times.
Gwamnatin Tinubu ta yi martani ga gwamnoni
Sai dai a martaninsa, Oyedele ya ce babu a matsala a lamarin inda ya ce suna kokarin tabbatar da adalci a lamarin harajin.
"Mun samu korafin gwamnonin Arewa kan rarraba tsarin harajin a kasa inda suke korafi kan rashin tsari da daidaito."
"Abin ya shafi dukan jihohin da ke yankunan kasar saboda an bi tsarin inda aka cire VAT madadin inda aka samar ko kuma batar da kaya."
- Mr Taiwo Oyedele
Gwamnoni sun bukaci ba sarakunan gargajiya dama
Kun ji cewa yayin taron gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya, an fitar da matsaya kan ba iyayen kasa dama a mulki.
Gwamnonin sun bukaci ba sarakunan gargajiya dama a kundin tsarin mulki domin ba da tasu gudunmawa wurin inganta kasa.
Hakan ya biyo bayan shiga ganawa ta musamman da gwamnonin suka yi da sarakunan gargajiya a jiya Laraba 30 ga watan Oktoban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng