'Yan Bindiga Sun Sace Manoma Suna Tsaka da Girbi a Gonakinsu
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari kan manoma a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Ƴan bindigan sun sace mutane 16 a harin da suka kai ƙauyen Bena na ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi
- Wasu daga cikin mutanen sun yi nasarar tserowa daga hannun ƴan bindigan yayin da aka yi kira ga gwamnati ta ƙara tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutane 16 a wani hari a jihar Kebbi.
Ƴan bindigan sun sace mutanen ne a wani hari da suka kai ƙauyen Bena da kewaye a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi.
Tashar Channels tv ta rahoto cewa sakataren kwamitin tsaro na Wasagu, Lawali Umar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Kebbi
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yi wa mutanen kwanton ɓauna ne lokacin da suke aiki a gonakinsu na dawa, sannan suka yi garkuwa da su.
Yayin da wasu daga cikin mutane 16 da aka yi garkuwa da su tun farko suka yi nasarar tserewa, kusan mutane tara har yanzu ana tsare da su, inda ƴan bindigan suka buƙaci a ba su kuɗin fansa.
Lawali Umar ya yi kira ga gwamnatin jihar Kebbi da ta ƙara tsaro a muhimman yankunan da ke fuskantar barazanar ƴan bindiga irinsu Ƴar Maitaba, Mai Rai Rai, da Tungar Sabo.
“Mun yaba da kokarin gwamnatin jiha kan yaƙi da ƴan bindiga, amma da zuwan lokacin girbin dawa yanzu, manoman mu na buƙatar ingantaccen tsaro."
- Lawali Umar
Ba a samun jin ta bakin ƴan sanda ba
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ba kan aukuwar lamarin.
Kakakin bai amsa kiran waya ba sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Ƴan bindiga sun kori mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla ƙauyuka 23 ne a ƙaramar hukumar Kontagora ta jihar Neja, ƴan bindiga suka kori mutanen da ke cikinsu.
Rahotanni sun ce ƙauyukan da abin ya shafa na cikin filin horas da sojoji a ƙaramar hukumar Kontagora, sai da hedikwatar tsaro ta karyata zancen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng