Sanusi Vs Aminu: Rikicin Sarautar Kano Ya Dawo, Kotu Ta Tanadi Hukunci kan Abubuwa 4
- Kotun ɗaukaka ƙara ta shirya yanke hukunci kan kararrakin da aka shigar gabanta game da rikicin sarautar Kano
- Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero na ci gaba da nuna kansu a matsayin sarakuna tun bayan sauya dokar masarauta
- Tun farko Gwamna Abba Kabir ya dawo da Sanusi II kan sarauta bayan rushe masarautu 5 da tsohon gwamna ya kirkiro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Har yanzu rigimar sarautar Kano ba ta wanye ba yayin da kotun ɗaukaka kara ta shirya yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafe huɗu da aka shigar gabanta.
Kotun mai zama a Abuja ta tanadi hukunci kan ƙararraki huɗu da aka ɗaukaka zuwa gabanta game da rikicin sarauta tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Daily Trust ta rahoto cewa kwamitin alkalan kotun ɗaukaka ƙara karkashin Mai Shari'a Mohammed Mustapha ne ya tanadi hukuncin a zaman ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da kowane ɓangare ranar da kotun za ta zauna don yanke hukunci kan shari'o'in sarautar Kano.
Yadda zaman kotun ɗaukaka ƙara ya kasance
Tun farko lauyan gwamnatin Kano, Adegboyega Awomolo (SAN) da lauyan majalisar dokokin jihar, Okechukwu Edeze (SAN) sun roki kotu ta amince da ƙararrakin da suka kawo.
Amma lauyan waɗanda ake ƙara P.H. Ogbole (SAN) ya bukaci kotun da ta yi watsi da duka ƙararrakin da ɓangaren gwamnatin Kano suka shigar.
Kotun ɗaukaka kara ta kori ƙorafi 3
Sai dai kotun ta yi fatali da wasu buƙatu uku da Alhaji Aminu Baba Dan Agundi ya kawo kan rashin cancantarsu da kuma yinkurin yi wa masu ƙara katsalandan.
Kazalika alkalin ya ci tarar Aminu Ɗanagundi N500,000 a kowace bukata, jimulla Naira miliyan 1.5 kenan.
Kararrakin da ke gaban kotun daukaka kara sun hada da shari'a tsakanin Alhaji Aminu Ado Bayero da Antoni Janar na Kano da wasu mutane 10 a kara mai lamba CA/KN/166/M/2014.
Sai kuma ƙara mai lamba CA/KN/126/M/2024 kan nadin sarkin Kano na 16 wanda ake fafatawa tsakanin majalisar dokoki da wani mutum guda da Aminu Ɗanagundi.
Gwamma Abba ya miƙa sanda ga sarkin Gaya
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mika sandar mulki ga Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim a ranar Lahadi.
Gwamnan na Kano ya bukaci sarkin da ya kasance abin koyi ga al'ummarsa tare da yin shugabanci bisa tafarkin addinin musulunci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng