Abin da Gwamnoni Suka Tattauna da Sarakunan Gargajiya, Sun Yi Musu Gata

Abin da Gwamnoni Suka Tattauna da Sarakunan Gargajiya, Sun Yi Musu Gata

  • An gudanar da wata ganawa ta musamman tsakanin sarakunan gargajiya da gwamnoni kan inganta shugabanci
  • Gwamnonin sun fitar da matsaya kan ba sarakunan gargajiya damar ba da gudunmawa a kundin tsarin mulki
  • A cewarsu, daukar matakin zai taimaka sosai wurin inganta shugabanci da samar da tsaro da kuma zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana abin da aka tattauna a ganawar gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya.

Yayin ganawar, gwamnoni da sarakunan gargajiya sun fitar da matsaya kan samarwa iyayen kasa ayyukansu na musamman.

Matsayar da gwamnoni da sarakunan gargajiya suka yi bayan ganawarsu
Gwamnoni sun bukaci ba sarakunan gargajiya dama domin ba da gudunmawarsu a hukumance. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Gwamnoni sun gana da sarakunan gargajiya a Abuja

Tribune ta tabbatar cewa an tattauna kan kudirin da ke gaban Majalisar Tarayya na ba su dama a kundin tsarin mulki domin ba da tasu gudunmawa.

Kara karanta wannan

Kuncin rayuwa: Gwamnoni, sarakuna sun shiga ganawa da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan gudunmawa da sarakunan ke bayarwa inda aka bukaci samar musu da gurbi a hukumance domin inganta zaman lafiya a kasa.

Shugaban zaman, Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya ce an yi ganawar domin kara samun haɗaka tsakaninsu, cewar rahoton Punch.

Gwamna AbdulRazak ya ce hadin kai a tsakanin bangarorin guda biyu zai yi matukar tasiri kan dakile matsalolin tsaro da inganta zaman lafiya.

Gwamna ya fadi tsarin ba sarakunan gargajiya dama

A bangarensa, Gwamna Dapo Abiodun na Ogun ya ce akwai bukatar ba sarakunan dama a kundin tsarin mulki domin ba da gudunmawa.

"Mun tattauna kan kudirin da ke gaban Majalisar Tarayya domin ba sarakunan gargajiya dama a harkokin gwamnati."
"Mai girma, Etsu na Nupe ya yi karin haske kan kudirin domin sarakunan gargajiya su shiga lamarin mulki da zaman lafiya da kuma tsaro."

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya dauki mataki da matashi ya yi zargin ya kware a neman mata

- Gwamna Dapo Abiodun

Gwamnoni, sarakunan gargajiya sun gana da Tinubu

A baya, kun ji cewa Gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya suna ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.

Ana hasashen cewa shugabannin suna ganawa ne domin neman mafita ga yan Najeriya kan halin da ake ciki musamman na tsadar rayuwa.

Lamarin ya biyo bayan wata ganawa da gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka yi ne a jihar Kaduna domin wasu matsaloli.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.