Jega Ya Tsage Gaskiya ga Gwamnatin Tinubu kan Biyewa Tsarin IMF

Jega Ya Tsage Gaskiya ga Gwamnatin Tinubu kan Biyewa Tsarin IMF

  • Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya a kan karɓar shawarwarin bankin duniya da IMF
  • Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa ya ce ba lallai ba ne duk abin da bankin duniya ko IMF suka fada ya zamo alheri ga yan Najeriya
  • Tsohon shugaban INEC kuma farfesan siyasa, Jega ya yi bayani ne yayin wani taro a da aka gudanar a yau Laraba, 30 ga watan Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan taka tsantsan da shawarwarin bankin duniya da IMF.

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa dole gwamnati ta kiyayi daukar matakin da zai iya jefa Najeriya a matsala.

Kara karanta wannan

“Za ku ji a jikinku:” Attahiru Jega ya fadi illar fita kasar waje saboda zafin talauci

Jega|Tinubu
Jega ya ba gwamnatin tarayya shawara kan IMF. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Farfesa Jega ya yi bayani ne yayin wani taro na musamman da cibiyar IOD ta shirya a yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IMF: Jega ya gargaɗi gwamnatin Tinubu

Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya bukaci gwamnatin tarayya ta rika taka tsantsan wajen yarda da tsare tsaren bankin duniya da IMF.

Jega ya bukaci a rika samar da shugabanci na gari a Najeriya maimakon sauraron shawara daga hukumomin Turai.

"Dole mu rika taka tsantsan wajen karɓar shawara daga gare su (Bankin duniya da IMF).
Idan ba mu yi taka tsantsan ba, za mu iya jefa kasar mu a matsala a gaba, hakan zai yiwu ko da muna ganin kamar muna cin riba a yanzu.
Bai kamata mu karbi dukkan abin da bankin duniya da IMF suka fada mana ba."

- Farfesa Attahiru Muhammad Jega

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Punch ta wallafa cewa Farfesa Jega ya ce babu laifi a rika tattaunawa da bankin duniya da IMF a kan wasu abubuwa amma ba wai a dauki duk abin da suka fada ba.

A makon da ya wuce, IMF ya musanta cewa shi ya ba Bola Tinubu shawarar cire tallafin man fetur a Najeriya.

Jega ya bukaci a zauna a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa sohon shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shawarci yan Najeriya da su dai na ficewa daga kasar.

Farfesa Jega ya ce fita kasar waje neman mafita ba shi ne maganin wahalar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin Najeriya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng