"Talauci Ya Fi Yawa a Arewa," Sabon Ministan Tinubu Ya Tsage Gaskiya a gaban Ƴan Majalisa
- Sabon ministan jin ƙai da yaki da talauci, Nentawe Yilwatda, ya ce talakawa sun fi yawa a Arewacin Najeriya fiye da kudu
- Da yake jawabi a majalisar dattawa, Yilwatda ya ce kaso 65% na talakawa ƴan Arewa ne don haka ya kamata a rika ware masu kaso mai tsoka
- Ya shaidawa sanatoci cewa idan ana son kawo karshen talauci a Najeriya sai an sauya tsarin yadda ake kasafta kuɗin shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗaya daga cikin mutanen da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa ministoci ya yi tsokaci kan talaucin ƴan Arewa.
Nentawe Yilwatda, wanda Tinubu ya naɗa a matsayin ministan harkokin jin ƙai ya shaidawa majalisar dattawa cewa talauci ya fi yawa a Arewacin Najeriya.
Sabon ministan ya faɗi haka ne da yake jawabi a gaban ƴan majalisar dattawa a lokacin tantancewa yau Laraba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arewa ta fi yawan talakawa a Najeriya
Yilwatda ya bayyana cewa kusan kashi 65% na talakawan Najeriya suna zaune ne a yankin Arewacin Najeriya, don haka ya kamata kason kudin yankin ya fi tsoka.
Da yake magana kan irin hanyoyin da ya kamata a bi domin kawar da talauci a Najeriya, Yilwatda ya ce:
"Kashi 65% na talakawan Najeriya ƴan Arewa ne, ragowar 35% ne suke zaune a Kudu, don haka ya kamata a zauna a duba abin da ake bukata a kowace ƙaramar hukuma ko jiha."
"Kamata ya yi a kasafta kuɗaɗen shiga daidai da talauci ko arzikin kowace jiha,."
Bayan ya yi wannan jawabi ne majalisar dattawan ta umarci ya rusuna kawai ya ƙara gaba.
Yilwatda zai maye gurbin Betta Edu
A makon da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya zabi Yilwatda a matsayin wanda zai maye gurbin Betta Edu, wacce aka dakatar kuma daga baya aka sallame ta.
Nan ba da jimawa ba majalisar za ta yanke shawara kan tabbatar da naɗin ministan ko akasin haka a zaman yau Laraba, 30 ga watan Oktoba.
Yadda majalisa ta fara tantance sababbin ministoci
A wani rahoton, an ji cewa majalisar dattawa ta amsa buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sababbin ministocin da ya naɗa a gwamnatinsa
Majalisar, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024 ta fara aikin tantance ministocin guda bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa.
Asali: Legit.ng