Majalisa Ta Fara Tantance Sababbin Ministocin Tinubu, an Samu Bayanai
- Majalisar dattawa ta amsa buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sababbin ministocin da ya naɗa a gwamnatinsa
- Majalisar a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024 ta fara aikin tantance ministocin guda bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa
- Naɗin na su dai na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul a makon da ya gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta fara tantance sababbin ministoci bakwai da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.
Ministocin dai an naɗa su ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa majalisar FEC garambawul ta hanyar sallamar wasu daga ciki.
Sababbin ministocin Tinubu sun bayyana a majalisa
Jaridar The Punch ta rahoto cewa an fara tantance ministocin ne bayan wani kuɗiri da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙudirin ya buƙaci majalisar ta dakatar da dokokinta domin ba mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin majalisa, Sanata Basheer Lado damar shigo da ministocin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta wasiƙar Shugaba Tinubu ta neman a tantance sababbin ministocin.
Bola Tinubu ya yi sababbin ministoci
Sababbin ministocin da aka naɗa sun haɗa da Nentawe Yilwatda ministan jin ƙai da rage talauci, Muhammadu Dingyadi a matsayin ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Bianca Ojukwu a matsayin ƙaramar ministar harkokin ƙasashen waje.
Sauran su ne Dakta Jumoke Oduwole ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Idi Muktar Maiha, ministan kiwon dabbobi, Yusuf Ata a matsayin ƙaramin ministan gidaje da raya birane, da Suwaiba Said Ahmad, ƙaramar ministar ilimi.
Tinubu ya aika saƙo ga ministocin da ya kora
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa ministocin da ya kora daga aiki bisa gudummuwar da suka ba gwamnatinsa da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙasar ya yi masu fatan alheri a dukkan lamurran da za su sa a gaba, ya ce Najeriya ba za ta manta da hidimar da suka yi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng