Yadda Rikicin Manyan Jam'iyyar APC Ya Fara Raba kan Sarakuna
- Rikicin manyan yan APC a Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda da Ibrahim Lamido ya fara shafar sarakunan gargajiya a jihar
- Rahotanni na nuni da cewa wasu sarakuna sun fara ajiye mukami domin bin wasu ɓangarorin yan siyasar APC a Sokoto
- Sanata Aliyu Magatakarda da Ibrahim Lamido na rigima a tsakaninsu ne saboda nuna karfin iko a kan jagorancin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Bincike ya nuna cewa rikicin manyan APC a Sokoto ya fara raba kan sarakunan gargajiya.
An fara samun sarakuna masu warewa gefe suna alakanta kansu da yan siyasa masu rikici a tsakaninsu.
Jaridar Daily Trust ta yi wani rahoto kan yadda rikicin Sanata Aliyu Magatakarda Wammako da Ibrahim Lamido ya fara shafar sarakuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin manyan yan APC a Sokoto
Manyan yan APC, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako da Sanata Ibrahim Lamido na rikici saboda nuna karfin iko.
Sanatocin suna ƙoƙarin nuna iko ne a kan jagorancin APC a Sokoto da kuma zama iyayen gida ga gwamnan jihar.
Rikicin APC ya fara raba sarakuna
Rikicin siyasa da ake a tsakanin manyan yan siyasar ya fara raba kan sarakunan gargajiya a Sokoto.
Sarkin Sabon Birni, Abdullahi Muhammad Bawa tare da wasu sarakunan gargajiya 19 sun fara mara baya ga bangaren Sanata Ibrahim Lamido.
Bayan haka, an samu masu rike da mukaman sarauta da dama da suka bayyana goyon baya ga Sanata Ibrahim Lamido, wasu kuma ga Aliyu Magatakarda.
Maganar APC a kan Ibrahim Lamido
Shugaban APC na Sokoto, Isa Sadiq Achida ya ce Sanata Ibrahim Lamido ba shi da wani tasiri a siyasar jihar.
Isa Sadiq Achida ya ce Sanata Ibrahim Lamido ya gaza cin zabe a mazabarsa balle ma ya kawo wani sauyi a siyasar Sokoto.
An karyata rasuwar sarkin Musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane da dama a Najeriya su na ta yada labarin cewa Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III ya rasu.
Sai dai fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta ƙaryata labarin inda ta ce Sultan yana nan lafiya babu abin da ya same shi zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng