Za a yi wa Yan Ta'adda Rubdugu, Najeriya da Saudiyya za Su Haɗa Kai

Za a yi wa Yan Ta'adda Rubdugu, Najeriya da Saudiyya za Su Haɗa Kai

  • Gwamnatin tarayya ta nuna amincewa da yin haɗaka da Saudiyya domin yaki da yan ta'adda a yankunan daban daban na Afrika
  • Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka yayin karɓar baƙuncin Manjo Janar Muhammad bin Saleem
  • Janar Muhammad bin Saleem ya zo Najeriya ne domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen yan ta'adda a yankin nahiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya nuna amincewa da haɗaka kan yakar yan ta'adda.

Cibiyar Musulunci da ke yaki da ta'addanci ta kasar Saudiyya (IMCTC) ce ta gana da ministan tsaron a Abuja.

Badaru
Najeriya za ta hada kai da Saudiyya kan tsaro. Hoto: Muhammad Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta ce a shirye ta ke wajen bayar da gudummawa kan tsaro a Afrika.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi luguden wuta kan Boko Haram suna tsaka da taro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya za ta yi haɗaka da Saudiyya

Punch ta wallafa cewa ministan tsoron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana amincewa da yin haɗaka da Saudiyya domin yakar ta'addanci a Afrika.

Muhammad Badaru ya bayyana haka ne yayin da cibiyar Saudiyya ta IMCTC mai yaki da ta'addanci ta kawo ziyara Najeriya.

"Muna shirye kuma za mu ba da gudunmawa domin cimma manufar yaki da ta'addanci a Afrika.
Lallai Afrika na fama da matsalolin yan ta'adda kuma za mu goyi bayan duk wani kokari da IMCTC ta kawo.
Lallai kasashen Afrika suna bukatar taimako kan matsalar tsaro."

-Muhammad Badaru Abubakar, ministan tsaro

Saudiyya na da alaƙa da Najeriya

Yayin jawabinsa, jagoran cibiyar IMCTC, Manjo Janar Muhammad bin Saleem ya ce tun asali Saudiyya na da alaƙa mai kyau da Najeriya.

Janar Muhammad bin Saleem ya ce sun kawo ziyarar ne domin karfafa alakar Najeriya da Saudiyya.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Hafsun tsaro ya ziyarci Nijar

A wani rahoton, kun ji cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ziyarci takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Janar Mousa Barmo.

Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya sanar da haka ga manema labarai a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng