Bankin Duniya: Za a Samu Saukin Abinci da Fetur, Amma Akwai Babban Kalubale
- Binciken Bankin Duniya ya bayyana cewa za a samu raguwar tashin farashin fetur da na abinci a wasu shekaru masu zuwa
- Raboton da Bankin ya fitar a ranar Talata ya nuna cewa za a samu saukin ne a a shekarun 2025 zuwa 2026 kafin farashin ya daidaita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar US - Bankin Duniya ya yi hasashen da zai shafi kasashen duniya a shekarun 2025 da 2026 a bangaren man fetur da kayan abinci.
Bankin ya bayyana cewa za a samu faduwar farashin kayan man fetur da dangoginsa da 6% a 2025, zai kuma kara faduwa da 2% a 2026.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa za a samu raguwar farashin kayan abinci a shekaru masu zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin Duniya ya yi hasashen saukin abinci
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Bankin Duniya ya yai hasashen za a samu raguwar farashin abinci a sassan duniya.
Rahoton Bankin ya bayyana cewa za samu raguwar farashin kayan abinci da 9% a shekarar 2024, sannan zai kara raguwa da 4% a 2025 kafin ya daidaita.
Bankin Duniya ya hango cikas kan farashi
Bankin Duniya ya ce ya hango babban kalubale ga saukar farashin man fetur da kayayyakin abinci da duniya za ta samu a nan gaba.
A rahoton da Bankin ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa za a samu karuwar tashe tashen hankula da yan bindiga za su haddasa.
Wannan matsala ta rashin tsaro za ta kawo cikas ga saukin kayan da ake sa ran samu.
"Babu dole:" Gwamnati kan shawarar Bankin Duniya
A baya mun wallafa cewa gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ba dole ba ne sai kasashe masu tasowa sun rika amfani da shawarwarin Bankin Duniya da na Asusun IMF ba.
Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana matsayar Najeriya a taron Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya su ka gudanar a Washington DC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng