Banki a Najeriya Ya Kara Cajin Hada Hadar Kudi, Ya Fitar da Bayanai

Banki a Najeriya Ya Kara Cajin Hada Hadar Kudi, Ya Fitar da Bayanai

  • Bankin Ecobank ya sanar da ƙara kuɗin hada-hada tsakanin bankin a Najeriya da na ƙasashen waje, ciki har da bankunan Afrika
  • Daga yanzu, abokan hulɗar bankin za su riƙa biyan $5 a kan duk hada-hadar da ke kasa da $200, idan ya haura haka za a biya $10
  • Fitaccen bankin na Afrika ya ce dole kamfanin ya kara kuɗin da ya ke karɓa bisa hada-hada duba da yadda kasuwanci ya sauya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ecobank ya bayyana yin ƙarin cajin da ya ka amsa a kan hada-hadar kuɗi da ta shafi ƙasashen ƙetare, har da bankunan da ke Afrika.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

Bayanin karin na ƙunshe a cikin sanarwar da bankin ya fitar ɗauke da sa hannun shugaban sashen biyan kuɗi, Adebayo Kejawa.

Banki
Ecobank ya kara cajin kudi kan hada-hada Hoto: Bloomberg/contributor
Asali: UGC

Legit ta tattaro cewa ƙarin zai fara aiki daga ranar Juma'a 1 Nuwamba, 2024 a kan duk hada-hada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bankin ya ƙara cajin hada-hada

Bankin Ecobank ya ce daga yau Juma'a, an kara cajin da ake karɓa a kan duk wata hada-hadar kuɗi da tsakaninsu da wasu bankuna a Afrika.

Za a riƙa biyan $5 a kan hada-hadar kuɗin ƙasa da $200, daga $200.1 zuwa $300, za a biya 0.5% na kuɗin ko $10, sai daga $300.1-$10,000 za a biya 0.5%.

Dalilin bankim na ƙara cajin hada-hada

Bankin yan kasuwa na Ecobank ya faɗi abin da ya tilasta masa ƙara kuɗin hada-hadar kasuwanci da abokan hulɗarsa.

Bankin ya ce an samu sauyi a yanayin cinikayya duba da yadda tattalin arziki ya sauya, saboda haka canjin da aka samu zai taimaka wajen gudanar da aikinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba da hutun kwanaki 2, ya bayyana dalili

IMF ta yabi tsarin bankin CBN

A baya mun ruwaito cewa asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana gamsuwa da yadda babban bankin Najeriya (CBN) ke tafiyar da harkokin tattalin arziki.

Mai ba da shawara kan harkokin kudi kuma darektan harkokin kuɗi na IMF, Tobias Adrian ne ya yi yabon bayan fadin yadda darajar Naira ke farfaɗowa a cewarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.