Gwamna Ya Fadi Rawar da Bangaren Shari'a Zai Taka wajen Magance Rashin Tsaro

Gwamna Ya Fadi Rawar da Bangaren Shari'a Zai Taka wajen Magance Rashin Tsaro

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya rantsar da alƙalin babbar kotun jihar Kaduna a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024
  • Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ɓangaren shari'a na da rawar da zai taka wajen murƙushe masu aikata laifuka
  • Ya buƙaci ɓangaren shari'a da ya daina jinkiri wajen hukunta mutanen da ake zargi da zama ƴan bindiga ko ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce ɓangaren shari’a na da muhimmiyar rawar da zai taka wajen ci gaba da yaƙi da rashin tsaro da gwamnati ke yi.

Gwamna Uba Sani ya bayyana jinkirin hukunta masu laifi ƙara musu ƙwarin gwiwar aikata laifuka ne.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun sanya labule da hafsun tsaro, sarakunan gargajiya

Uba Sani ya magantu kan rashin tsaro
Gwamna Uba Sani ya yi kira ga bangaren shari'a Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi yayin rantsar da wani alƙalin babbar kotun jihar, mai shari’a Murtala Zubairu a gidan gwamnatin jihar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya yi kira ga ɓangaren shari'a

Gwamnan ya bayyana cewa, domin gwamnati ta yi nasarar murƙushe masu aikata laifuka a jihar Kaduna yadda ya kamata, hukumomin da ke da alhakin gurfanar da su da kuma ɓangaren shari’a na da rawar da za su taka.

Gwamna Uba Sani ya ce dole ne su ba da fifiko kan tsaro tare da tabbatar da cewa ba a samu tsaiko ba wajen hukunta waɗanda ake zargi da zama ƴan bindiga da ƴan ta'adda.

Gwamnan ya yi alƙawarin inganta wuraren aiki na ma’aikatan shari’a, inganta amincewar jama'a ga ɓangaren shari'a, ƙara ba mutane damar neman haƙƙinsu a kotu da tura alƙalai zuwa ƙaro karatu, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fadi amfanin da zababbun ciyamomi za su yi a Kano

"A shirye na ke wajen inganta kyakkyawar alaƙar aiki tare da ɓangaren shari'a na."

Gwamna Uba Sani

Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba goyon bayan ɓangaren shari’a a duk hanyoyin da suka dace domin tabbatar da gudanar da adalci.

Gwamnan jihar Kaduna ya rage albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana matakan da ya ɗauka domin tsuke aljihun bakin gwamnati.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shi da ƴan majalisar zartaswarsa na karɓar rabin albashi da nufin rage kashe kuɗkn gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng