Tsadar Rayuwa: Gwamna Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Sani kan Halin Kunci a Najeriya
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya kare shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan
- Gwamna Sule ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana sane da halin ƙuncin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a gwamnatinsa
- Ya bayyana cewa wuyar da ake sha a halin yanzu a ƙasar nan ta wucin gadi ce domin abubuwa za su gyaru zuwa nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan tsadar rayuwa a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana sane da halin ƙuncin da ƴan Najeriya ke ciki sakamakon matakan da gwamnatinsa ta ɗauka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan hawansa kan mulki, Shugaba Tinubu ya ɗauki matakai masu tsauri da suka haɗa da cire tallafin mai da sakin Naira sakaka.
Waɗannan matakan sun sanya farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi wanda hakan ya jefa ƴan Najeriya cikin halin ƙunci.
Gwamna Sule ya kare Tinubu
Sai dai, Gwamna Sule ya ba da tabbacin cewa abubuwa za su gyaru zuwa nan gaba.
"Wasu daga cikin waɗannan matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka, ya fito ya bayyana cewa za a ga amfaninsu a nan gaba."
"A ɓangaren shugaban ƙasa, yana sane da waɗannan matakan. Babu wanda ya ce za su zo da sauƙi, tabbas za su yi tsauri. Wannan ita ce wuyar da za mu sha, amma ta wucin gadi ce."
- Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna ya gargaɗi ƴan APC kan Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya gargaɗi ƴaƴan APC su bar shugaban jam'iyyar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tunkari abubuwan da ke gabansa.
Gwamna Sule ya yi kashedin cewa bai kamata ƴaƴan APC su raba hankalin Ganduje ba a daidai lokacin da jam'iyyar ke tunkarar zaɓen gwamna a Ondo.
Asali: Legit.ng