Menene Gaskiyar Rade Radin Rasuwar Sarkin Musulmin Najeriya? Fadar Sultan Ta Yi Magana

Menene Gaskiyar Rade Radin Rasuwar Sarkin Musulmin Najeriya? Fadar Sultan Ta Yi Magana

  • Wasu mutane da dama a Najeriya su na ta yada labarin cewa Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III ya rasu
  • Sai dai fadar Sarkin Musulmi ta ƙaryata labarin inda ta ce Sultan yana nan lafiya babu abin da ya same shi zuwa yanzu
  • Har ila yau, ƙungiyar MPAC ta bukaci jami'an tsaro su dauki mataki kan masu yada irin wannan muguwar jita-jita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Fadar Sarkin Musulmai a Najeriya ta yi magana kan jita-jitar rasuwar Sarkin Musulmi da ake yaɗawa.

Fadar ta yi Allah wadai da jita-jitar da musanta labarin inda ta ce Mai Martaba, Sa'ad Abubakar yana cikin koshin lafiya.

Cibiyar Musulunci ta yi martani kan rade-radin rasuwar Sarkin Musulmi
An samu bayanai kan jita-jitar rasuwar Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar. Hoto: Nurphoto.
Asali: Getty Images

Sarkin Musulmi: Kungiya ta gargadi al'umma

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa, ya fadi abin da ya hana jihohin Arewa samun lantarki

Tun farko, shugaba kungiyar MPAC, Disu Kamor ya yi farali da labarin da ake ta yaɗawa kan rasuwar Mai Martaba, cewar New Telegraph.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamor ya ce lafiyar Sarkin Musulmi garau babu abin da yake damunsa a halin yanzu.

Kungiyar ta gargadi al'umma da su guji tafa jita-jita da kuma tantance labarin kafin fara yaɗawa.

Ta ce irin wadannan labarai marasa kan gado babu abin da za su kara illa rarrabuwar kawuna da kawo rudani.

Fadar Sultan ta magantu kan Sarkin Musulmi

Babban jami'i a fadar, Dr Muhammadu Jabbi Kilgori shi ya tabbatar da yayin hira da jaridar Daily Trust.

"Ba mu san menene suke son cimmawa da wannan jita-jitar ba, amma tabbas Sarkin Musulmi yana cikin koshin lafiya."
"Dazu ma muka bar jihar Kaduna domin halartar wani taro a birnin Tarayya Abuja kamar yadda ya saba."

Kara karanta wannan

'APC ta shiga uku': An ci gyaran Tinubu kan korar Minista, an fada masa illar hakan

- Muhammadu Jabbi Kilgori

Sarkin Musulmi ya fadi matsalolin Arewacin Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya koka kan matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya.

Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyana cewa wannan ƙalubalen shi ne abin da ya kamata shugabannin yankin su magance.

Ya nuna takaicinsa kan yadda miliyoyin yaran da ba su yin boko ke yawo a kan titunan garuruwa, birane da ƙauyuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.