Abin da Dangote Ya Gayawa Tinubu bayan Sun Sanya Labule a Aso Villa
- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi wata ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Dangote ya shaidawa Shugaba Tinubu cewa matatarsa za ta iya samar da man fetur ɗin da ake buƙata a ƙasar nan
- Dangote ya ce a yanzu haka yana da man fetur wanda zai wadaci ƙasar nan har zuwa nan da kwanaki 12 masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana yadda tattaunawarsu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, ta kaya.
Aliko Dangote ya gana da shugaba Bola Tinubu tare da sauran mambobin kwamitin sayar da ɗanyen man fetur a Naira.
Me Dangote ya gayawa Tinubu?
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Dangote ya ce ya shaidawa Shugaba Tinubu cewa matatarsa na da karfin samar da man da ke buƙata a ƙasar nan, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya yi ƙiyasin cewa ana buƙatar litar man fetur miliyan 30 zuwa 32 a kowace rana a Najeriya.
"Za mu iya samar da duk man da ake buƙata, abin da na yi ƙiyasi shi ne muna shan kusan lita miliyan 29-32."
"A yanzu da na ke magana da ku, muna da lita miliyan 500 a ma'ajiyarmu. Da hakan ko da ba mu ci gaba da samarwa ba ko ba a shigo da fetur ba, zai wadatar da ƙasar nan har zuwa nan da kwanaki 12."
"A shirye muke, kuma na gayawa shugaban ƙasa cewa za mu iya samar da fetur lita miliyan 30 kowace rana a kasuwa. Tabbas a shirye muke."
- Aliko Dangote
Ya bayyana cewa idan a yau aka dakatar da shigo da fetur da samar da shi a cikin gida, matatar Dangote na da ƙarfin da za ta kula da man da ake buƙata nan da kwanaki 12 masu zuwa.
Dangote ya magantu kan shigo da fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban matatar man Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatarsa ita ce mafita ga dogayen layukan man fetur da ake fama da su a fadin kasar nan.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya nemi Kamfanin an Fetur na Najeriya (NNPCL) da ‘yan kasuwa a fadin kasar da su daina shigo da mai daga ƙetare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng