Yan Bindigar da Suka Yi Garkuwa da Limami Sun Aiko Sako, Sun Nemi N200m

Yan Bindigar da Suka Yi Garkuwa da Limami Sun Aiko Sako, Sun Nemi N200m

  • Ƴan bindiga sun nemi a lale masu Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansar limamn cocin katolika da suka sace a Edo
  • A ranar Lahadi ne masu garkuwa suka yi awon gaba da Rabaran Thomas bayan sun yi yunkurin sace wasu ɗalibai biyu
  • Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun tuntuɓi cocin domin fara tattaunawar neman kudin fansa ranar Litinin dinnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da malamin cocin katolika, Rabaran Fr. Thomas Oyode sun buƙaci a biya N200m a matsayin kuɗin fansa.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da limamin cocin yayin da suka kai hari a makarantar Immaculate Conception Minor Seminary da ke ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a Edo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin rashin imani, sun yi wa bayin Allah yankar rago

Taswirar jihar Edo.
Masu garkuwa da limamin cocin Katolika na Edo sun bukaci a biya N200m Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Leadership ta tattaro cewa maharan sun sace Rabaran Thomas, wanda shi ne shugaban makarantar jim kaɗan bayan taron addu'o'in yammaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace limamin coci

Limamin cocin da kansa ya miƙa kansa ga ƴan bindiga domin su saki ɗaliban da suka sace daga makarantar ranar Lahadi.

Daraktan yaɗa labarai na cocin Katolika da ke Auchi, Rabaran Peter Egielewa ya tabbatar da cewa masu garkuwan sun kira sun nemi kuɗin fansa.

A wani saƙon kar-ta-kwana da ya aikawa manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, Egielewa ya ce, "Eh gaskiya ne, haka labarin yake,"

Ƴan bindiga sun nemi kuɗin fansa

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce a ranar Litinin, maharan sun tuntubi cocin Katolika ta Auchi, suka bukaci a ba su Naira miliyan 200 don fansar limamin.

Kara karanta wannan

Wani babban malami ya miƙa kansa ga ƴan bindiga, ya ceci ɗaliban da aka sace

"Har yanzun ba a fara tattauna kan kudin fansar da za a biya ba, kuma ba ni da masaniyar ko cocin katolika za ta biya fansar ko akasin haka," in ji shi.

Babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sandan reshen jihar Edo kan wannan harin har kawo yanzu.

Masu garkuwa sun shiga hannu

A wani rahoton na daban, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Delta ta yi nasarar cafke wani tsohon kansila bisa zarginsa da yunƙurin yin garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya sanar da cafke tsohon kansilan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262