'APC Ta Shiga Uku': An Ci Gyaran Tinubu kan Korar Minista, an Fada Masa Illar Hakan

'APC Ta Shiga Uku': An Ci Gyaran Tinubu kan Korar Minista, an Fada Masa Illar Hakan

  • Wata kungiyar matasan APC ta nuna damuwa kan sallamar tsohon karamin Ministan gidaje da raya birane
  • Kungiyar ta ce tabbas duk wanda ya ba Tinubu shawarar sallamar Abdullahi Gwarzo ya yaudari shugaban kasar
  • Hakan ya biyo bayan korar wasu daga cikin Ministoci da Bola Ahmed Tinubu ya yi a cikin makon da ya gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar matasa a Kano ta yi Allah wadai da korar Abdullahi Gwarzo daga mukaminsa na Minista.

Kungiyar mai suna The Congress of APC Youth Groups ta koka kan yadda aka kori tsohon karamin Ministan.

An soki Tinubu kan korar Minista, an fadi da zai yi wa APC
Matasan APC sun soki Bola Tinubu bayan korar Abdullahi Gwarzo daga mukaminsa. Hoto: @ATMgwarzo.
Asali: Twitter

An fadi illar da Bola Tinubu ya yi wa APC

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar PDP, jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamna

Shugaban kungiyar, Abdullahi Wada Kura shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Kano, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kura ya ce sallamar Gwarzo abin takaici ne kuma babban hatsari ne ga jam'iyyar APC musamman a jihar Kano baki daya.

Ya ce tabbas Gwarzo yana da al'umma sosai a jihar, ya kara da cewa sallamar shi a muƙamin, ya gigita mutane da dama.

Yadda korar Ministan Tinubu zai tarwatsa APC

"Ruwa Baba yana samun goyon bayan al'ummar jihar Kano da dama, korar shi a muƙamin ya kawo rudani a cikin al'umma."
"Wannan mataki har ila yau, zai raunana jam'iyyar APC a jihar da kuma tasirinta a nan gaba."

- Cewar sanarwar

Kungiyar ta ce korar Abdullahi Gwarzo siyasa ce kawai wanda wasu masu ƙarfi a Kano suka kitsa ta.

"Wanda ya kitsa korar Gwarzo tabbas ya yaudari shugaban kasa, mutum daya ba zai iya yanke shawara wa yan jiha ba."

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Ganduje ya fadawa yan Najeriya abin da ba su sani ba kan Tinubu

- Abdullahi Wada Kura

Abdullahi Gwarzo ya godewa Tinubu bayan korarsa

Kun ji cewa tsohon Minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya aika saƙo ga shugaban ƙasa Bola Tinubu bayan guguwar garambawul ta ritsa da shi.

Tsohon ƙaramin Ministan na gidaje da raya birane ya nuna godiyarsa ga shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba sa.

Ya yi fatan alheri tare da samun nasara ga wanda zai maye gurbinsa a kujerar da ya rasa a bayan taron FEC a makon da ya gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.