Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Aliko Dangote, an Samu Bayanai
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da kwamitin sayar da ɗanyen man fetur a Naira
- A wajen taron akwai Alhaji Aliko Dangote da dan kwamitin da yake ƙarƙashin jagorancin Wale Edun ne
- Ana sa ran a yayin taron Tinubu zai warware rikicin farashi da ake yi tsakanin matatar Dangote da NNPCL
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja -.Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya shiga ganawa da Aliko Dangote da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren harkai mai na ƙasar nan.
Shugaba Tinubu yana samun bayanai daga wajen kwamitin sayar da ɗanyen man fetur a Naira a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa, Abuja.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa mambobin kwamitin sun isa fadar shugaban ƙasan ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati na sayarwa Dangote fetur a Naira
Ministan kudi, Mista Wale Edun, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ne ke jagorantar tawagar da ta ƙunshi shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.
Akwai shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari a zaman.
A farkon watan Oktoba ne gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin sayar da ɗanyen man fetur ga matatar Dangote a Naira maimakon dalar Amurka.
Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar zartaswa ta tarayya inda ta ce tsarin zai daidaita farashin man fetur a cikin gida da kuma ƙarfafa kuɗin Najeriya ta hanyar rage buƙatar daloli a cinikin ɗanyen mai.
Matakin ya kuma ba kamfanin NNPCL damar samar da ɗanyen mai a Naira, inda matatar Dangote ke kan gaba wajen amfana da hakan.
Gwamnatin tarayya ta ce tsarin zai rage buƙatar kuɗin ƙasashen waje da kaso 40% yayin da manyan cibiyoyi da suka haɗa da babban bankin Najeriya (CBN) da kuma Afrexim Bank suka nuna goyon bayansu kan hakan.
Tinubu zai sasanta NNPCL da Dangote
Sai dai, a watan Satumba kamfanin NNPCL da matatar Dangote sun samu rikici kan farashin man fetur.
Ana sa ran a zaman, Shugaba Tinubu zai warware rikicin da ke tsakanin kamfanonin guda biyu.
Arziƙin Dangote ya ƙaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa arziƙin attajirin ɗan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote arzikin ya karu sosai daga dala biliyan 13 zuwa dala biliyan 27.8.
Rahotanni sun ce arzikin Dangote ya ninku ne a ƴan kwanakin nan bayan sabuwar matatar mansa da ya gina a Legas ta fara aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng