RCCG: An Dakatar da Manyan Malamai 2 kan Zargin Saɓon Allah, Za a Yi Bincike
- Cocin RCCG ta dakatar da wasu fastoci biyu bisa zarginsu da hannu a aikata babban laifin da ya saɓawa Littafi Mai Tsarki
- Ana zargin Fasto Ayorinde Ade Bello da Fasto Deacon Oke Mayowa da hannu a luwadi wanda RCCG ta ce ya saɓawa Injila
- A wata sanarwa da ta fitar, cocin ta ba da umarnin gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar wannan zargi da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Cocin RCCG ta dakatar da wasu fastoci guda biyu, Fasto Ayorinde AdeBello da Fasto Deacon Oke Mayowa bisa zarginsu da hannu a aikata luwaɗi.
Cocin ta sanar da dakatarwar ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 28 ga Oktoba, 2024, da kuma sa hannun Sunday Akande.
RCCG ta bada umarnin bincike
The Cable ta ce takardar da aka aikawa mataimaki na musamman ga shugaban cocin, ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa fastocin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ƙara da cewa cocin ba ta yarda ba kuma ba za ta taɓa lamuntar duk wani aiki na luwadi ba, yana mai nuni da nassoshi na Littafi Mai Tsarki watau Injila.
Sunday Akande ya ce a halin yanzun an sauke waɗanda ake zargin daga muƙamansu a cocin RCCG har sai an kammala bincike.
Cocin RCCG ya buƙaci a mutunta kowane ɓangare
Ya ce za a gudanar da binciken a tsawon makonni biyu kuma a asirce cikin gaskiya da kulawa tare da mutunta dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa.
"Wannan lamari ne mai girma da muhimmanci wanda ya kamata mu yi taka-tsan-tsan wajen warware shi da kiyaye ƙimar cocinmu."
"Muna fatan za a gudanar da wannan bincike cikin gaskiya da rikon amana tare da mutunta dukkan ɓangarorin da zargin luwaɗin ya shafa," in ji sanarwar.
Wani babban jami’in cocin ya tabbatar da sahihancin wasikar da dakatar da fastocin biyu a wani takaitaccen sako a ranar Talata, Leadership ta rahoto.
Kiristoci sun koka kan naɗe-naɗen NWDC
A wani rahoton, an ji cewa kiristoci a yankin Arewa maso Yamma sun nuna damuwa kan yadda aka yi wariya a mukaman hukumar NWDC.
Shugaban kungiyar CAN a yankin, Sunday Oibe ya ce an ware Kiristoci a hukumar raya yankin Arewa maso Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng