Rashin Wutar Lantarki: Yadda Masu Cajin Waya Ke Samun Kudi Masu Kauri

Rashin Wutar Lantarki: Yadda Masu Cajin Waya Ke Samun Kudi Masu Kauri

  • Matsalar rashin lantarkin da aka samu ta jefa jihohin Arewa da dama a cikin duhu yayin da harkokin kasuwanci suka samu tsaiko
  • Rashin wutar lantarkin dai ya jawo harkokin kasuwanci da dama sun tsaya cak, yayin da mutane suka yi ta tafka asara
  • Sai dai, a yayin da rashin wutan ya kawo tsaiko ga wasu harkokin kasuwanci, masu sana'ar cajin waya kakarsu ce ta yanke saƙa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Arewa - Yankin Arewacin Najeriya ya fuskanci matsalar rashin wutar lantarki ta tsawon wasu kwanaki bayan an samu wata matsala.

Ƙamarin da lamarin ya yi ya sanya harkokin kasuwanci da dama da suka dogara da wutar lantarki sun samu tangarɗa wajen gudanar da ayyukansu

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Gwamnatin Tinubu ta fadi lokacin gyara lantarkin Arewa

Masu cajin waya sun samu kudi a Arewa
Kasuwar cajin waya ta bude saboda rashin wutar lantarki a Arewa
Asali: Original

Wane ƙoƙari gwamnati ke yi kan lamarin

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ana kusa da gyara matsalar wutar lantarkin Arewacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan makamashin ya ba da tabbacin cewa nan da kwanaki uku masu zuwa za a maido da wutar lantarki a jihohin Arewa.

Adebayo Adelabu ya kuma ba da haƙuri kan lokacin da aka ɗauka ba tare da wutar lantarki ba a Arewacin Najeriya.

Kamfanin TCN ya ɗau damarar magance matsalar

Manajan hulda da jama'a na kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya ce Injiniyoyinsu na aiki tuƙuru domin dawo da hasken wutar lantarki Arewacin Najeriya, cewar rahoton tashar TVC News.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ndidi Mbah ya bayyana cewa tuni aiki ya yi nisa wajen magance kukan mazauna Arewacin ƙasar nan ta hanyar dawo da hasken wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi lokacin da za a maido wutar lantarki a jihohin Arewa

Masu sana'ar cajin waya sun dara

Sai dai, yayin da harkokin kasuwanci da dama suka samu matsala saboda rashin wutar lantarki, masu sana'ar cajin waya kakarsu ce ta yanke saƙa.

Masu sana'ar cajin wayar da Legit Hausa ta samu zantawa da su sun bayyana cewa sun samu riba sosai sakamakon rashin wutar lantarkin.

Sun ƙara da cewa shagunansu sun kasance babu masaka tsinke inda ake ta kawo wayoyi, fitilu, kwamfutoci tare da batura domin a caja su.

Umar Yusuf wani mai cajin waya a Katsina ya bayyana cewa ya samu kuɗi masu kauri a ƴan kwanakin da aka kwashe babu wutar lantarki.

"Eh a gaskiya a ƴan kwanakin nan na samu caji sosai, domin shagona sai da ya kasance yana cika maƙil da wayoyi da baturan mutane masu kawo caji."
"Na samu kuɗi sosai domin adadin cajin da ake kawowa ya ninka sau wajen huɗu zuwa biyar."

- Umar Yusuf

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun dunƙule, an miƙa dabarar magance matsalar lantarki ga Tinubu

Aliyu Abubakar ya bayyana cewa duk da dai cajin ya ƙara tsada saboda tsadar man fetur, ya samu kuɗi masu kauri sakamakon rashin wutar lantarkin.

"An samu kuɗi sosai a ƴan kwanakin nan, mutane sun kawo cajin wayoyi da batura saboda babu wutar lantarki."
"A kullum shagona cika yake da wayoyi, batura, fitilu da kwamfutoci na mutanen da suke kawo caji. Wasu ma ba su samun waje sai sun jira a layi tukunna saboda yadda wuraren suke cika."

- Aliyu Abubakar

TCN na ƙoƙarin gyara lantarkin Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce yana kan daukar matakai domin gyara wutar da ta lalace daga Shiroro zuwa Kaduna.

Kamfanin TCN ya bayyana cewa lalacewar layin wutar Shiroro ya janyo an samu daukewar wutar lantarki a Kaduna, Kano da sauran manyan biranen Arewacin Najeriya.

Manajar hulda da jama’a ta TCN, Ndidi Mbah, ta ce kamfanin na aiki tuƙuru domin gyara wutar cikin gaggawa duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng