Dan Majalisa Ya Kaskantar da Kai, Ya Nemi Afuwar Yan Najeriya kan Abin da Ya Yi

Dan Majalisa Ya Kaskantar da Kai, Ya Nemi Afuwar Yan Najeriya kan Abin da Ya Yi

  • Yayin da ake ta yin korafi kan cin zarafin wani direban tasi, dan Majalisar Tarayya a Najeriya ya nemi afuwa
  • Hon. Alex Ikwechegh ya ce ya yi nadamar aikata abin inda ya bukaci yafiya daga al'ummar kasar nan baki daya
  • Hakan ya biyo bayan zabgawa wani direba mari kan zargin mutumin bai mutunta shi ba a matsayinsa na dan Majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan Majalisar Tarayya a jihar Abia, Alex Ikwechegh ya yi magana bayan cin zarafin wani direba a Abuja.

Hon. Alex Ikwechegh ya nemi afuwar al'umma bayan zabgawa direban tasi, Stephen Abuwatseya mari.

Dan Majalisar Tarayya ya nemi afuwar yan Najeriya
Dan Majalisar Tarayya, Alex Ikwechegh ya yi nadamar marin direban tasi. Hoto: Alex Ikwechegh.
Asali: Facebook

Dan Majalisar Tarayya ya zabgawa talaka mari

Kara karanta wannan

'APC ta shiga uku': An ci gyaran Tinubu kan korar Minista, an fada masa illar hakan

TheCable ta ce Hon. Ikwechegh da ke wakiltar Aba ta Arewa da Kudu a jihar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan gaurawa diraban tasi mari inda dan Majalisar ya ke zarginsa da rashin mutunta shi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani mai tasi, Stephen Abuwatse ya kai kaya gidan dan Majalisar sai ya bukaci ya fito ya karbi kayan.

Fadin hakan ya sanya dan Majalisar ya ji kamar an raina shi har ya yi wa mai tasin barazana sosai.

Matakin dan Majalisar ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al'umma inda jami'an tsaro suka gayyace shi domin amsa tambayoyi.

Dan Majalisar Tarayya ya nemi yafiyar al'umma

Hon. Ikwechegh ya ce ya yi maganar abin da ya aikata cikin fushi inda ya nemi yafiyar al'umma gaba daya.

Kara karanta wannan

Shekaru 2 da mutuwar sarki, rigima ta tashi, an bukaci Gwamna ya kawo karshen rikicin

"Abin da ya faru kaman rashin jituwa ne ya koma rigima da aikata abin da bai dace ba."
"A matsayina na dan kasa kuma mai wakiltar al'umma bai kamata na yi haka ba."
"Ina neman afuwar abin dana aikata da kalamai na ya batawa al'umma da Abuwatseya da kuma iyalansa rai."

- Alex Ikwechegh

Dan Majalisar Abia ya musulunta

Mun ba ku labarin cewa dan Majalisar Tarayya, Alex Ifeanyi Ikwechegh ya bar addininsa, ya zama Musulmi kamar yadda wani ya yada a dandalin sada zumunta.

Mansur Ringim ya ce sun idar da sallah kenan a masallaci, sai ga ‘dan Majalisar yana kokarin karbar shahada a birnin Abuja.

Mutane musamman Musulmai sun yi farin ciki ganin yadda ‘dan Majalisar wakilan Tarayyar mai-ci ya rungumi addininsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.