Gwamnati Ta Fadi Lokacin da za a Maido Wutar Lantarki a Jihohin Arewa
- Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da za a maido wutar lantarki a jihohi 17 na Arewacin Najeriya da ke cikin duhu saboda rashin wuta
- Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa a yanzu haka sun dukufa wajen ganin komai ya kammala a kan gyaran lantarki a Arewa
- A yanzu haka dai an shiga rana ta tara tun da wutar lantarki ta dauke a mafi yawan jihohin Arewacin Najeriya ba tare da an gyara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya yi alkawari cewa ana kusa da kammala gyaran wutar lantarki a Arewa.
Adebayo Adelabu ya yi bayani ne jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Adebayo Adelabu ya ce akwai wasu shirye shirye da suke domin inganta wutar lantarki a jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a dawo da lantarki a Arewa?
Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa nan da kwanaki uku zuwa biyar za a kammala gyaran wutar Arewa.
Daily Post ta wallafa cewa Adebayo Adelabu ya ce a yanzu haka an dukufa wajen maido da lantarki a jihohi 17 na Arewacin Najeriya.
Ministan ya yi alkawarin ne bayan an shafe kwanaki tara babu wutar lantarki a mafi yawan jihohin Arewa.
"Idan aka samar da wadataccen tsaro, TCN da sauran ma'aikata za su kammala gyaran wutar a kankanin lokaci.
Kuma shugaban kasa ya bayar da umarnin gaggawa domin samar da tsaro a yankunan da za a yi gyaran."
- Adebayo Adelabu
Ministan wuta ya ba yan Arewa hakuri
Adebayo Adelabu ya yi kira ga yan Arewa da su kara hakuri kan kwanaki da suka dauka babu wutar lantarki.
Ministan ya tabbatar da cewa ba za a karbi kudin wuta a wajen mutane ba a tsawon kwanakin da aka shafe babu lantarki.
Rashin wuta ya durƙusa kasuwancin Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa rashin wutar lantarki ya jefa al'ummar Arewacin Najeriya a cikin matsalar tattalin arziki.
Yan kasuwa a Arewacin Najeriya sun bayyana yadda suka tafka asara a harkokin kasuwanci da sana'o'i musamman bayan shafe kwanaki takwas ba wuta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng