Shekaru 2 da Mutuwar Sarki, Rigima Ta Tashi, an Bukaci Gwamna Ya Kawo Karshen Rikicin

Shekaru 2 da Mutuwar Sarki, Rigima Ta Tashi, an Bukaci Gwamna Ya Kawo Karshen Rikicin

  • Yayin da ake cigaba da rigima kan sarautar Ikoyi-Ile da ke karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, kungiya ta ba gwamna shawara
  • Kungiyar ta bukaci Gwamna Seyi Makinde da ya sanya baki kan rigimar sarautar kada ta koma wani abu daban a jihar
  • Hakan ya biyo bayan mutuwar Oba Abdul-yekeen Ayinla Oladipupo a 2022 da aka maye gurbinsa da wasu ke ganin ba a bi ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - An bukaci Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ya saka baki kan rigimar sarauta da ke faruwa a jihar.

Kungiyar Ikoyi Land Vanguards ta bukaci Gwamna Makinde ya shiga lamarin sarautar Ikoyi-Ile

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya kaskantar da kai, ya nemi afuwar yan Najeriya kan abin da ya yi

An bukaci Gwamna ya sanya baki a rigimar sarauta da ake yi
An bukaci Gwamna Seyi Makinde ya kawo karshen rikicin sarauta na shekaru 2 da ake yi a Oyo. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Rikicin sarauta: An bukaci gwamna ya tsoma baki

The Nation ta ruwaito cewa kungiyar ta ce bukatar hakan ya zama dole duba da yadda lamarin ke gaban kotu domin tabbatar da gaskiya da adalci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce ta yi imanin cewa Gwamna Makinde yana da gaskiya da adalci tare da bin dokar kasa yadda ya kamata.

Hakan ya biyo bayan rigimar saurata kan kujerar Onikoyi na Ikoyi-Ile a jihar da har aka kwashe shekaru babu kowa a kanta.

Musabbabin jawo rigimar sarauta a Oyo

Farfesa Saka Jimoh shi ya zamo Sarkin bayan mutuwar Oba Abdul-yekeen Ayinla Oladipupo a shekarar 2022.

Sai dai wadanda suka nemi kujerar sarautar tare da Jimoh sun kawo wasu zarge-zarge da ke neman jawo rigima kan lamarin inda suka zargi cewa sabon Sarkin ba dan asalin Ikoyi-Ile ba ne.

Kara karanta wannan

Rigimar saurata ta barke, an gargadi Gwamna a Arewa kan tabbatar da sabon sarki

Shugaban kungiyar Ikoyi Land Vanguards, Taofeek Lawa ya ce dukan zarge-zargen da ake yaɗawa kan sabon sarkin karya ne.

Lawal ya ce suna da tarihin iyalan gidan Jimoh tun daga karni na 17 a Ikoyi-Ile suka yi rayuwa kuma suka mutu.

Sarakuna sun kai karar dan uwansu gaban gwamna

Kun ji cewa wani basarake ya shiga matsala bayan zarginsa da neman handame wasu filaye a jihar Osun da ke Kudancin Najeriya.

Ogiyan na Ejigbo, Oba Omowonuola Oyeyode ya kai karar Olusongbe na Songbe, Oba Kamilu Ojelabi gaban Gwamna Ademola Adeleke.

Wannan na zuwa ne yayin da gamayyar sarakuna 19 suka bukaci gwamnan ya yi bincike kan matsalar filaye da ake zargin basarake.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.