Matsin Rayuwa: Ganduje Ya Fadawa Yan Najeriya Abin da ba Su Sani ba kan Tinubu

Matsin Rayuwa: Ganduje Ya Fadawa Yan Najeriya Abin da ba Su Sani ba kan Tinubu

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai bukatar jama'a su marawa Bola Ahmed Tinubu baya
  • Ya ce gwamnatin tarayya ta na iya bakin kokarinta domin magance matsalar tattalin arziki da ta dabaibaye yan Najeriya da gaske
  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tura sako ga jama'ar Ondo kan zaben gwamnan jihar da ke tafe a ranar 16 Nuwamba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa yan Najeriya kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi kan tattalin arziki.

Ganduje ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya na kokari matuka wajen kawo karshen wahalar da jama'ar kasar nan ke ciki a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan jami'a da suka shiga yajin aiki sun kawo sharadin komawa ofis

Ganduje
Ganduje ya ce Tinubu ya na kokarin magance matsalar kasar nan Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ganduje ya fadi haka ne a Akure bayan kaddamar da kwamitin mutum 305 na yakin neman zaben gwamnan Ondo da zai gudana ranar 16 Nuwamba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya nemawa Tinubu goyon baya

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai bukatar mazauna Kudu maso Yamma su marawa Bola Tinubu baya saboda manufofinsa masu kyau.

Ya ce dadin dadawa, Tinubu ya fito daga yankin, wanda shi ma dalili ne mai kyau da ya cancanci goyon bayan mazauna shiyyar.

Ganduje na son APC ta rike mulkin Ondo

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya nemi kwamitin yakin neman zaben Ondo su tabbata an kawo kujerar gwamnan Ondo a zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa kamata ya yi a yi wa shugaban kasa, Bola Tinubu kara wajen tabbatar da cewa APC ta ci gaba da mulki a jihar.

Kara karanta wannan

Kusa a PDP ya soki Tinubu kan kyale Mawatalle a mukaminsa, ya fadi illar haka

Ganduje ya yi magana neman kujerar Tinubu

A wani labarin kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, kuma tsohon gwamnan Kano sau biyu, Abdullahi Umar Ganduje ya musanta labarin da ke cewa ya na hararar kujerar shugaban kasa a 2027.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zargi magoya bayan tafiyar Kwankwasiya da yada fastoci da ke nuna shi da gwamnan Imo a matsayin masu neman takarar shugaban kasa da mataimakinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.