'Zan Dauwamar da Talauci': Kwamishina a Arewa Ya Yi Katobara, an Taso Shi a Gaba

'Zan Dauwamar da Talauci': Kwamishina a Arewa Ya Yi Katobara, an Taso Shi a Gaba

  • Al'umma da dama a jihar Taraba sun caccaki wani kwamishina kan furucin da ya yi a kasar China wanda suke ganin abin takaici ne
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, an gano kwamishina, Habu James Philip yana cewa zai tabbatar da talauci a jihar
  • Hakan ya jawo cece-kuce cikin al'umma musamman yan jihar da ke ganin ya kamata Gwamna Agbu Kefas ya yi gaggawar daukar mataki kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - An dira kan wani kwamishina a jihar Taraba bayan katobarar da ya yi a ketare game da talauci.

Kwamishinan hadin kai da rage radadin fatara, Habu James Philip ya jawo cece-kuce ne a lokacin wani taro a China.

Kara karanta wannan

'APC ta shiga uku': An ci gyaran Tinubu kan korar Minista, an fada masa illar hakan

Kwamishina a Taraba ya kawo cece-kuce a cikin al'umma
Wasu yan jihar Taraba sun taso kwamishina a gaba kan katobarar da ya yi. Hoto: Agbu Kefas.
Asali: Twitter

Taraba: Kwamishina ya jawowa kansa jarfa

Punch ta ce kwamishinan yayin taron ya ce ya samo wasu dabarun da za su tabbatar da talauci a cikin al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan furuci ya jawo ka-ce-na-ce da har wasu ke neman Gwamna Agbu Kefas ya dakatar da shi saboda kalaman cin fuska ne.

Wani ma'aikaci a jihar Taraba, Sulaiman Usman ya ce wannan abin takaici ne a matsayinsa na wanda ake sa ran zai gigita talauci a jihar, cewar Tribune.

"Wannan abin kunya ne ga al'ummar jihar, ta yaya wanda ake tsammanin zai yaki talauci kuma ya ce zai tabbatar da dorewarta?"

- Suleiman Usman

Mene hadimin gwamna ya ce kan lamarin?

Sai dai hadimin gwamnan jihar a bangaren sadarwa ta zamani, Hon. Emma Bello ya yi martani kan lamarin.

"Ina ganin wannan ba wani abu ba ne illa tuntuben harshe saboda Gwamna Kefas yana iya kokarin dakile talauci a jihar Taraba."

Kara karanta wannan

An bi gida gida, an kashe mutane a rikicin manoma da makiyaya

- Hon. Emma Bello

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane sun fusata da furucin kuma za su cigaba da matsawa har sai an cire kwamishinan daga mukaminsa.

Dan takarar gwamna a APC ya kwafsa

Kun ji cewa an yi ta cece-kuce bayan kuskuren da dan takarar gwamna APC a jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi yayin kamfe.

An gudanar da kamfe din ne a karamar hukumar Ovia ta Arewa da ke jihar inda Okpebholo ya tafka kuskure.

Yayin kamfen, Okpebholo ya yi wa yan jihar alkawarin zai kawo musu 'rashin tsaro' wanda kowa ya sha mamaki a lokacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.