Bayan Arewa Ta Shafe Sama da Mako 1 a Duhu, Tinubu Ya Ba da Umarnin Gaggawa

Bayan Arewa Ta Shafe Sama da Mako 1 a Duhu, Tinubu Ya Ba da Umarnin Gaggawa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar wutar lantarki a Arewa bayan jama'a sun shafe kwanaki babu haske
  • A sakon da hadiminsa ya fitar a ranar Litinin, Bola Tinubu ya ce bai ji dadin yadda aka samu rashin wuta a Arewa ba
  • Ya ba Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da sauran jami'ai umarnin gaggauta warware matsalar da ta jawo rashin wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Bayan jihohin Arewacin Najeriya sun kwana akalla takwas babu ko kyallin hasken wutar lantarki, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni

Shugaba Tinubu ya ce bai ji dadin yadda layin da ke kai hasken wutar lantarki ya lalace har ta kai ga samun gagarumar matsalar rashin wuta ba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 8 a duhu: Yadda rashin wuta ke durƙusar da kasuwanci da sana'o'i a Arewa

Tinubu
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gyara wutar Arewa Hoto: Kinga Krzeminska
Asali: Facebook

A sakon da hadiminsa kan yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X, shugaban ya fara jagorantar kawo karshen matsalar cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kadu da lalata layin lantarki

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, hadimin shugaba Tinubu kan yada labarai, Bayo Onanuga ya ce tuni shugaban kasa ya ba Ministan makamashi umarnin gaggauta gyara wutar Arewa.

Shugaban ya bayyana takaici kan rahoton da ya samu na lalata layin wutar lantarki da ya jawo rashin wuta da lalacewar kadarori a jihohin Arewacin Najeriya.

Tinubu ya ba da umarnin gyara lantarki

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta magance layin wutar lantarkin sa ya samu matsala,wanda jefa yan Arewa a cikin duhu.

Tinubu ya nemi Injiniyoyin da ke gyaran wutar da su rubanya kokarin da su ke yi domin farfaɗo da tattalin arzikin mutanen yankin.

Kara karanta wannan

Ana bakin kokari, TCN ya fadi lokacin dawowar hasken lantarki a Arewa

Arewa: TCN ya ce ana gyara lantarki

A baya mun ruwaito cewa kamfanin hasken wutar lantarki na ƙasa (TCN) ya shaidawa yan Najeriya, musamman na Arewa cewa ana can ana kokarin gyara wutar lantarki.

Layin lantarki da ke kawo hasken wuta Arewacin Najeriya ya samu matsala kimanin kwanaki takwas da su ka wuce, kuma har yanzu TCN ta ce ana kokarin gyara shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.