Yadda Bola Tinubu Ya Nuna Fifiko, Ya Naɗa Ministoci 4 daga Jiha 1 a Yankin Yarbawa

Yadda Bola Tinubu Ya Nuna Fifiko, Ya Naɗa Ministoci 4 daga Jiha 1 a Yankin Yarbawa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba da mamaki bayan nada ministoci guda hudu daga jiha daya da ke Kudu maso Yammacin kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Hankalin jama'a ya fara karkata kan nadin ne bayan garambawul da shugaban kasar ya yi wa gwamnatinsa, inda ake ganin ya karkata zuwa jihar Ogun.

A wancan lokaci ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Minista ta hudu daga jihar Ogun, Dr Jumoke Oduwole, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Minista
Tinubu ya naɗa ministoci4 daga Ondo Hoto: Nigerian Senate/Bosun Tijani/Iziak Kunle Salako
Asali: Facebook

Legit ta tattaro Ministocin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ya nada daga jihar Ogun da kuma ma'aikatun da su ke kula da su a wannan rahoto;

Kara karanta wannan

Gwamna ya fara garambawul, ya kori shugaban jami'a da wasu manyan jami'ai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Wale Edun: Ministan kudi da tsare tsare

Adebayo Olawale Edun dan asalin jihar Ogun ne da aka fara gwamnatin Bola Tinubu da shi a matsayin Ministan tattalin arziki da tsare-tsare na kasa.

A shekarar 2023 da aka naɗa shi Minista ne aka ba shi shugaban kungiyar Gwamnonin Afrika na Bankin Duniya a 2023, shi ne dan Najeriya na farko da ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a cikin shekaru 60.

A shekarar 1999-2004, Wale Edun ya riƙe muƙamin kwamishinan kudi a Legas, lokacin Bola Tinubu ya na a matsayin gwamnan jihar.

2. An naɗa ɗan jihar Ogun a kujerar ƙaramin Minista

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Iziaq Adekunle Salako a matsayin ƙaramin Ministan Muhalli na ƙasa tun a farkon gwamnatinsa.

An haifi Dr. Salako a ranar 9 ga Agusta 1967 a yankin Ayetoro Yewa ta Arewa, jihar Ogun, kuma ƙwararren likita ne da ya yi shura a fanninsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi rigakafi, ya nemi kotu ta shiga tsakinsa da EFCC tun kafin ya bar ofis

Gabanin naɗa shi Minista a gwamnatin Tinubu, ya rike mukamai daban-daban kamar na shugaban hukumar kula da manyan asibitoci a jihar Ogun daga 2020-2023.

Daktan ya kuma rike mukamin kwamishinan lafiya na jihar Ogun daga shekarar 2007-2011.

3. Bosun Tijani ya zama Ministan sadarwa

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Bosun Tijani a matsayin Ministan tattalin arzikin zamani, sadarwa da kirkire-kirkire.

An haife shi a ranar 20 Yuli, 1977 a Agege da ke jihar Legas inda ya fara karatunsa, daga nan ya shiga Jami'ar Jos kuma ya fara da karatun Diploma.

Bosun Tijani ya koma Kasar Ingila inda ya cigaba da samun takardar kammala jami'a a fannin tattalin arziki a shekarar 2002.

Daga bisani a dora da samun ilimi a fannoni da dama kamar bangaren sadarwa da cinikayya.

4. Ogun: Oduwole ta zama Minista ta 4

A ranar 30 Oktoba, 2024 majalisar Najeriya ta tabbatar da Dr Jumoke Oduwole a matsayin Minista a gwamnatin Tinubu, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Ganduje ya fadawa yan Najeriya abin da ba su sani ba kan Tinubu

A matsayintan na Minista ta huɗu daga jihar Ogun, Jumoke Oduwole za ta jagoranci ma'aikatar ciniki da zuba jari.

Kafin tabbatar da ita a ranar Talata, Dr. Oduwole mai ba shugaban kasa shawara ce a kan harkokin zuba jari.

Sannan ta rike mukamin mai ba Muhammadu Buhari shawara kan masana'antu, kasuwanci da zuba jari a shekarar 2015-2023.

Majalisa ta tabbatar da ministocin Tinubu

A wani labarin kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da sababbin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayensu domin a tantance.

Bayan ganawa da ministocin yayin tantance su a ranar Laraba, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce sun gamsu da mutanen da Tinubu ya zabo.

Ministocin da aka tantance sun hada da Yusuf Ata, Idi Mukhtar Maiha, Suwaiba Sa'id Ahmad, Jumoke Oduwole, Muhammadu Dingyadi, Nentawe Goshwe Yilwatda da Bianca Ojukwu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.