An Cafke Dan Majalisar da Ya Gaggaurawa Talaka Mari a Abuja

An Cafke Dan Majalisar da Ya Gaggaurawa Talaka Mari a Abuja

  • Rahotanni na cewa rundunar yan sanda a birnin tarayya Abuja ta cafke wani dan majalisar wakilai bisa zargin cin zarafi
  • An ruwaito cewa dan majalisar, Alexander Mascot ya lakaɗawa wani matukin motar tasi duka bayan sun samu sabani
  • Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun yawaita kira ga yan sanda su cafke dan majalisar biyo bayan faruwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar yan sanda birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke dan majalisar wakilai, Hon. Alexander Mascot Ikwechegh.

An kama dan majalisar ne biyo bayan duka da ya yiwa wani mai tuka motar haya a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

‘Ba a son ranmu ba ne': Mabarata ga Ministan Tinubu da yake shirin fatattakarsu

Dan majalisa
An kama dan majalisa a Abuja. Hoto: Hon. Alex Ifeanyi Ikwechegh
Asali: Facebook

Rahoton Channels Television ya nuna cewa a yanzu haka ana yi wa dan majalisar tambayoyi a caji ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya haɗa dan majalisa da mai tasi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani mai tasi, Stephen Abuwatseye kai kaya gidan dan majalisar sai ya bukaci ya fito ya karbi kayan.

Fadin hakan ya sanya dan majalisar ya ji kamar an raina shi har ya yi wa mai tasi din barazana sosai.

Dan majalisa ya mari mai tasi a Abuja

Biyo bayan fitowar dan majalisar ya wanke mai tasi din da mari sau biyu, bayan ya yi magana ya kara masa daya.

Dan majalisar ya kuma fadawa mai tasi din cewa ya je ya yi duk abin da zai yi, idan ya so ya kira sufeton yan sandan Najeriya.

Yan sanda sun kama ɗan majalisa

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Biyo bayan lamarin, mai tasin ya wuce caji ofis domin sanar da yan sanda abin da ya faru a a tsakaninsu.

Rundunar yan sanda ta bi diddigin abin da ya faru wanda daga baya ta cafke dan majalisar da ake zargin.

Kakakin yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta bayyana cewa a yanzu haka dan majalisar yana amsa tambayoyi.

Yan sanda sun kama mai gadi

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Legas na nuna an kama wani mai gadin maƙabarta da ake zargi ya haɗa kai da wasu miyagun mutane.

Ana zargin cewa mai gadin maƙabartar na hada kai da wasu mutane wajen sace sassan jikin wadanda suka mutu, aka birne su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng