Hamshakin Attajiri, Ɗantata da Tsohon Ministan Tinubu Sun Faɗa Hannun Ƴan Damfara
- Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin ɗaurin watanni shida kan mutanen da aka kama da laifin damfarar Aminu Ɗantata da Abdullahi T. Gwarzo
- Kotun mai zama a Gyadi-Gyadi ta ce ta samu Bukar Galadima da Suleiman Ahmed da laifin haɗa baki da aikata rashin gaskiya
- Rahotanni sun ce masu laifin sun karɓi N5m daga hannun Ɗantata ta hanyar amfani da sunan tsohon minista, Injiniya Abba Gama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Wasu mutum biyu da suka damfari hamshakin attajirin nan, Alhaji Aminu Ɗantata da tsohon minista, Abdullahi T. Gwarzo sun girbi abin da suka shuka.
Wata kotun majistire mai zama a Gyadi-Gyaɗi a cikin jihar Kano ta yanke wa mutanen biyu hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.
Mutanen dai su ne Bukar Galadima da Suleiman Ahmed, waɗanda kotun ta kama su da laifin yunkurin damfara, rahoton jaridar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka damfari Ɗantata da T. Gwarzo
Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun haɗa kai, suka karɓi Naira miliyan 5 daga wurin Ɗantata da Naira miliyan ɗaya daga hannun T. Gwarzo.
Ɗaya daga cikinsu ya yi kama da tsohon minista, Injiniya Abba Gama, wannan damar suka yi amfani da ita suka karbi N5m daga wurin Ɗantata.
Alhaji Ɗantata ya ba mutumin tallafin N5m saboda ya faɗa masa ba shi da lafiya, ya ɗauka tsohon ministan ne amma daga baya ya gano damfara ce.
Hamshakin attajirin ya kai ƙara hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano, wanda bayan gudanar da bincike ta cafke Galadima da Ahmed.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Bayan sauraron bayanan kowane ɓangare a shari'ar, alkalin kotun, Umma Sani Kurawa ta ce ta samu waɗanda ake tuhuma da laifin haɗa baki da aikata rashin gaskiya.
Alkalin ta yanke musu hukuncin ɗaurin watanni shida ko tarar N30,000 da ɗaurin watanni uku ko tarar N20,000.
Bugu da ƙari, Mai shari'a Umma Sani ta yankewa mutanen biyu hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari ko biyan tarar N20,000 bisa aikata laifin rashin gaskiya.
Shekarau ya gana da tsohon ministan Tinubu
A wani rahoton kuma Malam Ibrahim Shekarau ya gana da karamin ministan gidaje da raya birane da shugaba Bola Tinubu ya kora, Abdullahi Tijjani Gwarzo
Wata sanarwa da Abdullahi Gwarzo ya fitar ta nuna cewa tsohon gwamnan Kano ya gana da tsohon ministan domin taya shi murna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng