“Za Ku Ji a Jikinku:” Attahiru Jega Ya Fadi Illar Fita Kasar Waje saboda Zafin Talauci

“Za Ku Ji a Jikinku:” Attahiru Jega Ya Fadi Illar Fita Kasar Waje saboda Zafin Talauci

  • Tsohon shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shawarci yan Najeriya da su dai na ficewa daga kasar
  • Farfesa Jega ya ce fita kasar waje neman mafita ba shi ne maganin wahalar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin Najeriya ba
  • Ya shawarci jama’a kan matakan da ya dace su dauka wajen gina kasarsu, ba wai a bar ta zuwa kasashen da su ka gina kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce fita kasashen waje saboda wahalar rayuwa ba mafita ba ce.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ragargaji Tinubu, ya fadi yadda rashin wuta zai yi wa Arewa

Farfesa Jega ya bayyana haka a taron sake fasalta Najeriya da ya gudana a Abuja, inda ya ce neman sauki a kasashen waje ba mafita ba ne.

Farfesa
Attahiru Jega ya shawarci yan kasa kan fita ci rani Hoto: Willy Ibimina Jim-george/Swasti Mehul Jain
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa tsohon shugaban INEC ya kara da shawartar yan Najeriya kan matakan da ya kamata su dauka na magance matsalar talauci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jega ya shawarci yan Najeriya kan fita waje

Jaridar This day ta tattaro tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce mafi yawan yan kasar nan da ke fita neman arziki a kasashen waje na fadawa cikin nadama.

Ya ce yawancin mutanen Najeriya da ke fita kasashen waje su na kokarin dawowa gida, saboda haka ne ya shawarci jama’a kan su zauna a gina kasar tare.

“Kasashen waje suna wahala:” Jega

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa sauran kasashen waje da ake yi wa kallon masu arziki yanzu sun sha wahala kafin su kai matakin da su ke kai.

Kara karanta wannan

"Ban da APC:" KANSIEC ta fadi jam'iyyun da ke takara a zaben Kano

Tsohon shugaban na INEC ya fadi fatansa na cewa wata rana, kasar nan za ta kai matakin cigaban da kowa zai yi alfahari da ita.

“Rashin wuta zai jefa jama’a talauci:” Obi

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya koka kan yadda rashin wutar lantarki a Arewacin kasar nan ke barazanar kara talauci.

Obi ya fadi haka ne yayin da mazauna shiyyar Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa maso Tsakiya su ka tsunduma a cikin duhu har da sama da mako guda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.