Sarkin Musulmi Ya Fadi Babban Kalubalen Shugabannin Arewa

Sarkin Musulmi Ya Fadi Babban Kalubalen Shugabannin Arewa

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya koka kan matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya
  • Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyana cewa wannan ƙalubalen shi ne abin da ya kamata shugabannin yankin su magance
  • Ya nuna takaicinsa kan yadda miliyoyin yaran da ba su yin boko ke yawo a kan titunan garuruwa, birane da ƙauyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa batun almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta, babban ƙalubale ne ga shugabanni a Arewacin Najeriya.

Sarkin Musulmi ya nuna cewa akwai miliyoyin irin waɗannan yara da suke yawo a garuruwa, birane da ƙauyuka a faɗin yankin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun sanya labule da hafsun tsaro, sarakunan gargajiya

Sarkin Musulmi ya fadi matsalar Arewa
Sarkin Musulmi ya bukaci shugabanni su magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Sultan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ƙungiyar gwamnonin Arewa a wani taro da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya ba gwamnoni shawara

Mai alfarma ya buƙaci gwamnonin da su sanya wannan batu a tattaunawarsu, ya jaddada buƙatar magance matsalar a yankin.

Sarkin Musulmin ya ci gaba da cewa a matsayinsu na shugabanni za su goyi bayan kafa hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin domin ganin an samu nasara.

"Batun yaran da ba su zuwa makaranta da Almajirai babbar matsala ce a gare mu baki ɗaya. Idan ka zagaye jihohi, garuruwa, birane da ƙauyuka, abin da za ka gani ba shi da kyawun gani."
"Muna da ɗaruruwan yara, idan ba dubbai ko miliyoyi ba da suke yawo. Wajibi ne mu goyi bayan wannan hukumar domin ta samu nasara."

Kara karanta wannan

"Na yi shekara 3 da rabi a cikin mahaifiyata": Tsohon gwamna ya fadi abin al'ajabi

"Na tabbata idan ta yi nasara, duk za mu ce eh tabbas muna kan hanyar samun ƴanci. Da zarar ka ilimantar da wani, ka ba shi ƴancin zama kansa, ya yi wa kansa aiki, ya yi wa al'umma aiki."

- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya ba yan Najeriya shawara kan abin da ya kamata su rika yi wa shugabanninsu.

Mai alfarman ce sam babu kyau wadanda ake jagoranta su rika fadin munanan kalamai a kan shugabanninsu duk da lalacewar tattalin arziƙi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng