Wani Babban Malami Ya Miƙa Kansa ga Ƴan Bindiga, Ya Ceci Ɗaliban da Aka Sace

Wani Babban Malami Ya Miƙa Kansa ga Ƴan Bindiga, Ya Ceci Ɗaliban da Aka Sace

  • Wani malamin cocin Katolika ya miƙa kansa ga ƴan bindiga domin ceton ɗalibai biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Edo
  • Rahotanni sun nuna maharan sun yi yunkurin sace ɗaliban amma limamin cocin ya roki su sake su, su tafi da shi a madadinsu
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Edo ya ce suna kan hanyar zuwa wurin da lamarin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika mai suna Rabaran Thomas Oyode a ranar Lahadin da ta gabata a Edo.

Lamarin ya faru ne a makarantar Immaculate Conception Minor Seminary School a Agenegbode, karamar hukumar Etsako ta Gabas ta jihar Edo.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun sanya labule da hafsun tsaro, sarakunan gargajiya

Taswirar jihar Edo.
Limamin Katolika ya bada kansa don ceton ɗalibai 2 da aka yi garkuwa da su a Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wata majiya ta faɗawa Leadership cewa ‘yan bindigar sun farmaki makarantar ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda fasto ya miƙa kansa ga ƴan bindiga

A cewar majiyar, ƙarar harbe-harben bindigar ne ya ja hankalin malamin cocin ya fito daga gida yana tunanin masu gadi ne don ya ja masu kunne.

"Lokacin da Rabaran Thomas ya fito babu-zato sai ya taras da ƴan bindiga sun ɗauki dalibai biyu a makarantar suna koƙarin tafiya da su.
"Ganin haka ne malamin wanda shi ne shugaban makarantar ya roki maharan su saki ɗaliban, su tafi da shi a maimakonsu.
"Kuma haka aka yi, suka saki ɗaliban suka tafi da malamin cikin daji,"

- Majiyar

Cocin katolika ta tabbatar da faruwar lamarin

Cocin katolika da ke Auchi ta tabbatar da garkuwa da faston a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Rabaran Peter Egielewa ya fitar.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani babban malami a Najeriya

Egielewa ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari makarantar cocin a lokacin da ake addu’o'in yammaci misalin karfe 7 na daren ranar Lahadi.

Ya ce maharan sun yi nasarar tafiya da shugaɓan makarantar, Rabaran Oyede zuwa cikin daji, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo, SP Moses Yamu, ya ce suna kan hanyar zuwa wurin da lamarin ya faru. 

Ƴan bindiga sun sace limami a Anambra

A wani labarin kuma ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin coci a Awkuzu da ke ƙaramar hukumar Oyi ta jihar Anambra a shiyyar Kudu maso Gabas.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi awon gaba da faston a ƙofar shiga cocin ranar Asabar da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262