Tinubu Ya Sanya Labule da Kashim Shettima, An Samu Bayanai

Tinubu Ya Sanya Labule da Kashim Shettima, An Samu Bayanai

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gana da Shugaba Bola Tinubu a ofishinsa da ke fadar Aso Rock a birnin tarayya Abuja
  • Kashim Shettima ya yi wa Shugaba Tinubu bayanin halin da ƙasar nan take ciki yayin da ya tafi hutun makonni biyu a ƙasashen waje
  • Ganawar ta su na zuwa ne bayan mataimakin shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya bayan ya yi wata tafiya zuwa ƙasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bayanin halin da ƙasa ke ciki a lokacin hutun makonni biyu da ya tafi.

Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma yi wa Tinubu bayani kan tafiyarsa zuwa ƙasar Sweden inda ya wakilci shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa kansa a matsayin Minista? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya gana da Shettima
Tinubu ya gana da Shettima a ofishinsa Hoto: @DOlusegun, @ƘashimSM
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Bola Tinubu ya gana da mataimakin shugaban ƙasan ne a ofishinsa a ranar, Litinin, 28 ga watan Oktoban 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu da Shettima sun je ƙasar waje

A ranar 2 ga watan Oktoba ne dai shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa ƙasar Ingila domin yin hutu na makonni biyu.

Kafin Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya, Kashim Shettima ya je ziyarar kwanaki biyu a ƙasar Sweden.

A ranar 19 ga watan Oktoba, 2024, shugaba Tinubu ya dawo Najeriya bayan hutun makonni biyu a Birtaniya da Faransa.

Shugaba Tinubu ya buƙaci Shettima da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kasashen rainon Ingila wanda da aka gudanar a Samoa.

Sai dai, Shettima bai samu damar yin hakan ba sakamakon wani abu da ya samu jirginsa a birnin New York.

Kashim Shettima ya dawo Najeriya yayin da tawagar ministocin ta halarci taron.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Fadar shugaban kasa ta fadi matsayin ministar da Tinubu ya dakatar

An buƙaci a sayowa Shettima sabon jirgi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce rayuwar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima na cikin haɗari.

Shugaban majalisar ya ce rayuwar Shettima na cikin haɗari ne sakamakon lalataccen jirgin shugaban ƙasa da yake amfani da shi wajen wakiltar shugaba Bola Tinubu a wajen taruka a faɗin duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng