Betta Edu Ta Faɗi Abin da Ta Hango a Mulkin Tinubu bayan An Koreta daga Minista

Betta Edu Ta Faɗi Abin da Ta Hango a Mulkin Tinubu bayan An Koreta daga Minista

  • Betta Edu ta bayyana cewa tana da ƙwarin guiwar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai sabunta burin ƴan Najeriya
  • Tsohuwar ministan jin kai ta buƙaci ƴan Najeriya su ƙara hakuri, duk matsin nan zai zama tarihi nan ba da daɗewa ba
  • Wannan dai na zuwa ne bayan fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da korar Betta Edu da Tinbu ya dakatar tun a watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohuwar ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Betta Edu ta ce Najeriya na cikin wani yanayi amma nan ba da dadewa ba komai zai wanye.

Betta Edu ta ce tana da yakinin cewa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu za ta kai ‘yan Najeriya zuwa tudun mun tsira.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa kansa a matsayin Minista? Gaskiya ta bayyana

Bola Tinubu da Betta Edu.
Betta Edu ta bai wa ƴan Najeriya hakuri, ta ce Bola Tinubu zai tsame su daga halin kunci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Betta Edu
Asali: Facebook

Edu ta bayyana haka ne a ranar Lahadi a Abuja a wurin bikin cikarta shekaru 38 da haihuwa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Betta Edu ta roki ƴan Najeriya su kara haƙuri

Tsohuwar ministar ta ƙara rarrashin ƴan Najeriya kan halin matsin da ake ciki, inda ta roke su da su ƙara hakuri.

"Ina ƙara godewa Allah, ina gode muku bisa yadda kuka nuna mun kauna tare da tallafawa matasa. Zan yi amfani da wannan damar wajen yi wa kasarmu addu’a don ina da yakinin cewa Najeriya za ta inganta.
"Ina da yaƙinin burin ƴan Najeriya zai dawo kuma Allah zai ba shugaban ƙasa kuma jagoranmu, Bola Ahmed Tinubu hikima da basirar tafiyar da ƙasar nan.
"Haka nan kuma ina da tabbacin cewa abubuwa za su sauya, bayan wuya sai daɗi. Babu abin da zance face ƴan Najeriya su ƙara haƙuri, komai zai wuce, za mu fita daga wannan kangin kowa zai ji daɗi."

Kara karanta wannan

Betta Edu: Fadar shugaban kasa ta fadi matsayin ministar da Tinubu ya dakatar

- Betta Edu.

Hadimin Tinubu ya tabbatar da korar Edu

Wannan kalamai dai na zuwa ne bayan fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da korar Betta Edu daga matsayin ministar harkokin jin ƙai.

Tun farko, Shugaba Tinubu ya dakatar da Edu ne a watan Janairu, 2024 bisa zargin karkatar da Naira miliyan 585 a ma'aikatarta.

T-pain: Fadar shuaban ƙasa ta yi martani

A wani rahoton kuma hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu yana sane da halin da ƴan Najeriya suke ciki

Onanuga ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba T-pain ba ne kamar yadda wasu suke yi masa laƙabi a kafafen sada zumunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262