Ana Bakin Kokari, TCN Ya Fadi Lokacin Dawowar Hasken Lantarki a Arewa
- Kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya karyata cewa za a dade kafin a gyara wutar Arewa da ta lalace kwanaki takwas baya
- Manajan hulda da jama'a na kamfanin, Ndidi Mbah ya sanar da cewa tuni ma'aikatansu su ka yi nisa wajen aikin gyaran matsalar
- Ya bayyana cewa rahoton da ake yadawa na babu lokacin gyaran lantarkin ba shi da tushe ballantana makama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kamfanin Wutar Lantarkin Najeriya (TCN), ya musanta cewa babu ranar gyara wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Bayanin ya biyo bayan rahotanni da ka cewa matsalar wuta a Arewa sai abin da hali ya yi bayan shafe kwanski takwas babu ko kyallin hasken wutar lantarki a shiyyar.
A sakon da TCN ya wallafa a shafinsa na X, kamfanin ya bayyana cewa an fahimci zancen guda daga cikin Injiniyoyinsa, Nafisatu Ali ba daidai ba bayan ta ce yan ta'adda ne su ka lalata turakun wutar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TCN ya ce ana gyaran lantarki
Kafar TVC ta ruwaito cewa Manajan hulda da jama'a na kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya ce Injiniyoyinsu na aiki tukuru domin dawo da hasken lantarki Arewacin Najeriya.
A sanarwar da ya fitar, ya ce tuni aiki ya yi nisa wajen sada mazauna Arewacin kasar nan da hasken wutar lantarki a yan kwanakin nan.
Yadda TCN ke gyaran lantarki a Arewa
Kamfanin TCN ya bayyana cewa a halin da ake ciki, ya na aiki da ofishin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro domin gyara layin wutar lantarki da ya lalace.
Sanarwar da TCN ta fitar ta ce hakan ya zama dole domin bayar da tsaro ga ma'aikatan da ke aikin gyara turakun lantarkin da ke kawo wuta Arewa.
TCN ya fadi dalilin lalacewar lantarki
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin wuta na kasa (TCN) ya ce wutar lantarki ta lalace a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Tsakiya da Arewa maso Gabas a Najeriya.
Manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya tabbatar da cewa wasu layukan wuta da ke kan tashar Ugwaji-Apir ne suka samu matsala amma an aika ma'aikata domin gyara su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng